Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wani ɗan kasuwa mai shekaru 52 a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA) bisa zargin safarar hodar iblis.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja ta tabbatar da kama wanda ake zargin, bayan isowarsa daga Bangkok, Thailand, ta jirgin Ethiopian Airlines (ET 941) a ranar Laraba, bisa bayanan sirri da hukumar ta samu tun da wuri.
Babafemi ya ce, bayan an gudanar da binciken jiki da duban na’ura, an gano cewa wanda ake zargin ya haɗiye hodar iblis kuma ya ɓoye wasu a sassan jikinsa.
“An fara gano ƙulli 58 na hodar iblis a cikin wandonsa, sannan aka ci gaba da lura da shi har ya fitar da ƙarin 69 a lokuta daban-daban, inda jimillar ta kai ƙulli 127 masu nauyin kusan kilogiram 1.388,” inji sanarwar.
Hukumar ta bayyana cewa wanda ake zargin yana da shagunan sayar da kaya a Legas da Onitsha kafin aka kama shi.
A wani ɓangare kuma, jami’an NDLEA a Legas sun kama wasu kayan ƙwayoyi da ake shirin aikawa ƙasashen waje.
Daga cikin su akwai kilo 1.7 na kwayar methamphetamine da aka ɓoye cikin tubalan gilashi, da kuma allurai 114g da 168g na pentazocine da tramadol, tare da wasu 48g da aka ɓoye a cikin akwati na ɓitamin C, duk ana shirin aikawa Birtaniya.
Har ila yau, hukumar ta ce an katse yunƙurin wasu da ke shirin tura 2.6kg na tabar skunk da 422g na tapentadol 250mg zuwa Turkiyya, da kuma 169g na hodar iblis da aka ɓoye cikin jakar mace zuwa Ostiraliya.
Haka kuma an gano 568g na tabar wiwi mai ƙarfi (Loud) da aka ɓoye cikin akwatunan ganyayyaki zuwa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
NDLEA ta ce tana ci gaba da tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen sama da wuraren aikawa da kaya, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai domin hana masu safarar miyagun ƙwayoyi samun nasara.
