Tarihin Hawan Sallah a Ƙasar Hausa (II)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yau za mu cigaba da kawo tarihin hawan sallah na masarauto daban-daban daga inda muka tsaya a makon da ya gabata.

Masarautar Gwandu:

Hawan Sallah a Masarautar Gwandu ya samo asali da daɗewa tun zamanin sarakuna kuma an fara ne bayan Jihadi kamar yadda Alhaji Ibrahim Baisat, Galadiman Gwandu ya shaida.

Yayin hawan idi da ƙaramar sallah, uwayen ƙasa na ƙasar Gwandu 15 duk suna zuwa da dawakai 30 ko 40 wasu ma 50.

A cewarsa, ana gudanar da hawan farko bayan sallar idi. “Idan aka (idar) da idi, ana fara kiɗi, lokacin kakaki su jira sai Sarki ya hau, ‘yan sarki su hau, yaran sarki su hau,”

“Suna jeruwa ne bi da bi kuma suma uwayen ƙasa suna bi tare da dawakansu kuma wanda ke ƙarshe shi ɗan sarki ne da ake kira Uban Doma.” kamar yadda ya faɗa.

Savanin wasu daga cikin Masarautun Ƙasar Hausa da suke gudanar da hawan bariki, Masarautar Sarki ba ta yin wannan hawa illa “hanyar da sarki ya sani ita ake bi a shigo cikin gari.”

“Mutane su taho bakin hanya ana girgiza ana hawam shi kuma sarki yana amsawa.” a faɗin Galadiman Gwandu.

Idan kuma Sarki ya isa fada daga masallaci, sarki yana tsayawa ya fuskanci yamma don karɓar gaisuwa, kuma masu jiran sarauta su ke fara kai gaisuwa domin a san suna nan da biyayya.”

“Daga nan kuma sai yaran sarki sai uwayen qasa, idan an gama, Sarki kuma sai ya yi jawabi ya shiga gida,” a cewar Galadiman Gwandu.

Sai dai kuma, acewarsa, akwai ɗan banbanci a lokacin hawa da sallar inda ɗan sarki ɗaya ne ke tahowa da dawaki su hau.

“Sauran uwayen ƙasa an basu dama su tsaya garinsu su yi nasu ikon, amma gaisuwar sallah ba a ɗauke musu ba.”

Masarautar Katsina:

A Katsina, ana yin hawa sau biyu da ƙaramar sallah, sannan da babbar sallah ma a yi hawa guda biyu savanin wasu masarautun da ke hawa da yawa.

Hawan Idi:

A cewar Alhaji Bello Mamman Ifo, Sallaman Katsina kuma Sakatare na Masarautar Katsina, a baya ana yin hawa sau ɗaya wato hawan idi.

A wannan hawa, mai martaba yana fitowa daga gida ya bi ta hanyar Guga domin ya dawo gida – tsarin da ake yi kafin zuwan Turawa.

Sai dai ya ce hawa ya sauya a yanzu inda aka ƙara hawa ɗaya wanda, “idan aka yi hawan idi a yau, gwamna Bature zai zo fadar Sarki ya yi masa gaisuwar sallah.”

Mai martaba yana fita ne da safe, “ya bi ta ƙofar Guga zuwa masallacin idi wanda ke bisa hanyar Jibia daga Katsina, idan aka idar kuma zai biyo ta hanyar ƙofar ‘yan Ɗaka ya sake zagayowa ya dawo kan filin Kangiwa inda ake kira ƙofar soro, zai iske dukkan hakimansa suna jiransa wanda suma tuni sun zo kan dawakansu suna jira.

“Amma Sarki shi ne a ƙarshen tawaga yayin da Mai girma Ƙauran Katsina shi ne a gaba sai ‘Yan Ɗakan Katsina, Galadiman Katsina da Durɓin Katsina sune a jerin gaba sannan sauran hakimai za su biyo baya,” a cewar Alhaji Bello Mamman Ifo.

Hawan Sarki:

A cewar Sallaman Katsina “Kwana ɗaya da idi kuma mai martaba zai yi hawan Sarki ko hawan Barki inda zai iske Gwamna Bature su gaisa, idan ƙaramar sallah ce su yi wa juna barka da shan ruwa.”

“Idan kuma babbar sallah ce su yi wa juna barka da saukowa daga Arfah.

Masarautar Kazaure:

A wannan masarauta ana yin hawan sallah guda uku

Hawan Idi:

Bashir Hussaini Adamu, Ɗan Amar ɗin Kazaure ya ce yayin wannan hawa, Sarki yana fita daga fada zai ɗauki hanya zai je masallacin idi, tafiya masallacin hanya biyu ake bi hanyar da aka tafi ba ita ake dawowa ba.”

“Zai zagaya ta kudun gari tun da masallaci na gabas, zai yi kudu daga fadarsa ya karkata ya zagaya kamar kudun gari ya shiga masallaci can gabas da gari.”

“Idan an taso kuma zai dawo ta arewa da gari ya dawo ƙofar fada inda za a yi ɗan hawa ba mai yawa ba.”

A cewarsa, babu wasu bukukuwa tattare da wannan hawa sai dai zuwa masallaci.

Hawan Bariki:

Ana yin wannan hawa ne ranar biyu ga sallah kuma asalinsa shi ne sarki yana hawa tun zamanin Turawan mulkin mallaka, yana zuwa wajen gwamna Bature su gaisa,

“Yana bi ta hanyoyi daban-daban domin zagaye gari, a dawo fada, ya karvi gaisuwa sannan ya yi jawabi,” in ji Ɗan Amar ɗin Kazaure.

Ya ce, an fi daɗewa a wannan hawa.
Hawan Daushe

Ana gudanar da wannan hawa da yamma a rana ta uku ga sallah.

A wannan ranar, “bayan la’asar kowane hakimi akwai yaransa, ɗa jika ko jika ko ɗan ɗan uwa, daga gidan Sarki ma za a samu yaro shi ne zai wakilci sarki a ranar – yana iya zama ɗan sarki ko jikansa ko ɗan ɗan uwansa.”

“Hakimai suma za su sa wakilansu, kuma da zagagensu har ‘yan bindiga ma yara ne.”

A cewarsa, ana zaɓar ‘ya’yan da za su wakilci Sarki, suna juyawa ne a tsakaninsu.”

Sai dai ya ce zagayen da suke a wannan hawa bai kai na sarki ba.

Masarautar Bauchi:

Kamar wasu daga cikin Masarautun Ƙasar Hausa, a wannan Masarautar ma, irin bukukuwan hawan sallar da ake gudanarwa sun zo kusan ɗaya a cewar Ado Ɗanrimi Garba, Wakilin Tarihin Bauchi.

Ya ce, ana gudanar da hawan sallah lokacin ƙarama da kuma babbar sallah. Hawan sallar da ake yi a Bauchi sun haɗa da:

Hawan Sallah ƙarama da babba.

“Shi wannan hawa ana yinsa ne bayan saukowa daga sallar idi, kuma Sarki na bi ne ta Ƙofar Wambai daga nan za a sa lema da tambari sannan ya wuce titin unguwar jaki sannan ya dawo ƙofar fada inda zai karɓi gaisuwa.”

“Amma da kafin Sarki Musa Adamu Jumɓa. lokacin Sarkin Bauchi Yakuba Ɗan Umaru akan tsaya a ƙofar saraki ne sa fito daga masallacin idi sai tsaya a karɓi jahi, sai kuma sarki ya yi jawabi ko huɗuba ga jama’a,” in ji Ɗanrimi Garba.

Hawan Bariki:

A cewar wakilin tarihin Bauchin, “a da ana shigowa hawan bariki wato hawan da ake washegarin sallah akan shigo ne da sallar layya kasancewar idan an shigo baƙi kan shigo da dabbobinsu su yanka gari ya yi wari yana damun mutane.”

“Saboda tsaftar gari, sai aka ce sallar layya kowane hakimi ya zauna ya yi a garinsa sannan a riqa shigowa da sallar azumi,” kamar yadda wakilin tarihin ya faɗa.

A wannan hawan ne Sarki ya ke kai ziyara gidan gwamnati inda ya ke gabatar da hakimansa tare da yin jawabi. Daga baya shi ma gwamna yana yin jawabi a ranar.

Ado Ɗanrimi Garba ya bayyana cewa, an fara wannan hawa ne tun a shekarar 1914 lokacin da Turawa suka zo su yi kallon hawan sallah.

Masarautar Borno:

Game da sanin hawan da ake yi a Masarautar Borno, mun yi ta yunƙurin samun bayanai kan hakan amma ba mu samu sahihan bayanai daga masarautar ba.