Tarihin wasu muhimman abubuwan da suka faru a Musulunci cikin watan Ramadan

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ga Musulmin duniya, watan Ramadan, wata ne mai alfarma kuma wanda abubuwa suka faru a cikin watan tarihin Musulunci.

Ramadan wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna Ibadar azumi, ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci.

Baya ga kasancewa watan Ibadah, abubuwan tarihi da dama sun faru a cikin Ramadan, wanda shi ne wata na tara a kalandar Musulunci.

Jaridar Blueprint Manhaja za ta kawo wasu muhimman abubuwan da suka faru a watan Ramadan, duk da cewa akwai abubuwa da dama na tarihi da suka faru a watan mai alfarma.

Saukar da Al-Ƙur’ani:

Babban muhimmin abu da ya faru a watan Ramadan, kuma mafi muhimmanci ga Musulmi a watan shi ne saukar da Al Ƙur’ani mai tsarki ga Annabi Muhammad (SAWW).

Allah ya bayar da labarin saukar da Al Kur’ai kuma an fara saukar da Al Kur’ani ne a daren Laylatul Ƙadr a watan Ramadan.

Daren Laylatul-Ƙadr a watan Ramadan darajarsa ta fi ta wata dubu.

Yaƙin Badar;

Yaƙin Badar ya faru ne a ranar 17 ga watan Ramadan, shekara biyu bayan Hijrar Manzon Allah daga Makkah zuwa Madina.

A yaƙin ne Musulmi suka yi nasara, duk da maƙiya sun fi su yawa.

Sahabban Annabi 14 ne suka yi shahada a ranar.

A yaƙin ne aka kashe Abu Jahl, ɗaya daga cikin manyan maƙiyan manzon Allah.

Ƙwace Makkah:

Shekara takwas bayan Hijra a ranar 18 ga Ramadan Annabi SAWW ya shiga Makkah tare da runduna domin karɓe ikon Makkah, wanda kuma aka yi nasara cikin lumana, duk da cewa ba a yi fito na fito ba.

Kama wannan ne ya kawo ƙarshen bautar gumaka a Makkah, ɗaya daga cikin lokuta mafi muhimmanci a tarihin addinin Islama.
Mutane da dama ne suka karɓi addinin Musulunci bayan samun nasarar.

Rasuwar Nana Khadija (AS);

Nana Khadija (AS) ta rasu ne a ranar 10 ga watan Ramadana.

Ita ce matar Manzon Allah ta farko, uwa ga Sayyida Fatima Az-Zahra (AS) kuma ta farko da ta karɓi addinin Musulunci.

Ta kasance mafi ƙarfi da goyon baya ga kafuwar Musulunci.

Rasuwar Nana Aisha RA:

A ciki shekara ta 58 bayan Hijra, Nana Aisha RA matar Manzon Allah ta rasu.

Ta rasu ne 17 ga watan a Ramadan.

Ta taka muhimmiyyar rawa a Musulunci. Wasu malamai sun tafi akan cewa kashi ɗaya bisa huɗu na koyarwar Musulunci Nana ‘Aisha RA ce ta ruwaito.

Shahadar Sayyidina Ali (AS):

A ranar 19 ga watan Ramadan aka sari Imam Ali Ibn Abi Talib (AS) da takobi.

Ya yi shahada ne a ranar 21 ga Ramadan shekara 40 bayan Hijrah saboda raunin da ya samu daga harin da aka kai masa.

Tun a daren ranar 19 ga watan Ramadana shekara ta 40 bayan hijira, Bin Muljam ya nufi masallacin Kufa yana mai dakon isowar Amirul Muminina don ba da sallar asubahi.

To daman tun da jimawa Amirul Muminina (a.s) ya bayyana shahadar tasa a wannan rana, don daman Manzon Allah (s) ya masa bayanin hakan, don haka a wannan ranar ma da zai fita sallar asubahi sai ya ce wa ‘ya’yayensa (Imam Hasan da Husaini) da su zauna a gida, kada su biyo shi masallaci kamar yadda suka saba. An ruwaito cewa lokacin da ya shirya zai fita hatta dabbobin da suke gidan sai da suka ta kuka, koda masu aikin gidan suka yi ƙoƙarin hana su, sai Amirul Muminina ya ce, su barsu ba komai su ke yi ba face suna juyayin mutuwarsa ne.

Koda ya isa masallaci ya kira salla, kana kuma ya fara jagorancin mutane a sallar, sai wannan la’anannen Allah (Abdurrahman bn Muljam) wanda da man ya samu wuri a sahun gaba sai ya taso ya sari Amirul Muminina a kansa, sara mai tsanani da takobinsa mai tsananin guba a jiki. Nan take Amirul Muminina ya fadi cikin jini, kamar yadda da man Manzon Allah (s) ya gaya masa wata cewa: “Ya Ali! An nuna min yadda wannan gemu naka zai jika da jinin kanka”.

Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!, kalmar farko da ta fara fita a bakin Amirul Muminina (a.s) ita ce Fuztu wa Rabbil Ka’aba”, wallahi na sami babban rabo.

Nan take dai sahabban Amirul Muminin suka kame wannan la’anannen Allah, yayin da ya ke ƙoƙarin gudu bayan ya aikata wannan ɗanyen aiki, a ka kawo shi gaban Amirul Muminin. Koda ya ga irin tsananin ɗaurin da aka yi wa Abdurrahman ɗin, sai ya buƙaci da a sassauta masa kuma a yi masa mu’amala mai kyau. Ganin irin wannan ɗabi’a ta kwarai, sai ya (Abdurrahman bn Muljam) ya fara kuka, sai Amirul Muminin ya ce masa “Ai lokaci ya ƙure maka na tuba, don ka riga da ka aikata abin da ka aikata….”.

Daga nan sai Amirul Muminin ya ba da umurnin cewa kada a ƙuntata wa wannan makashi nasa, kada a azabtar da shi, kada a lalata gawarsa bayan kashe shi, kada a ƙuntata wa iyalansa saboda wannan aiki da ya yi, haka nan kuma kada a ce za a kwace dukiyarsa. Allahu Akbar! adalcin Amirul Muminina ba wai kawai ya tsaya ga masoyansa ba ne hatta ma ga maƙiyansa.

Imam Ali ya saura yana fama da jinya har na tsawon kwanaki uku har zuwa lokacin da ya yi shahada a ranar 21 ga watan Ramalana mai albarka, shekara ta 40 bayan hijira. A cikin waɗannan kwanakin ya miƙa akalar Imamanci ga ɗansa Hasan a bayan shi, don ya ɗauki ɗawainiyar jagorancin al’umma, ya kuma ci gaba da tafiyar da Imamanci a bayan shi.

An kashe Imam (a.s) a lokacin yana mafificin lokaci da ya ke tsaye a gaban Allah a cikin sallarsa mai cike da kaskantar da ki ga Allah Maɗaukaki; a cikin mafi ɗaukakar ranaku, domin yana ɗauke da azumin watan Ramadan; a lokacin yana cikin aiwatar da mafi girman taklifin Musulunci, wato yana kan hanyarsa ta jihadi; kamar yadda ya kasance a wani lungunan Allah Maɗaukaki kuma mafi tsarkin su (wato masallancin Kufa).

Wannan aika-aika ba wai ta nufi wani mutum ne kamar sauran mutane ba; a’a ta nufi shugabancin Musulunci ne bayan Annabi (s.a.w.a), ta kuma nufi kashe saqo, tarihi, wayewa da al’umma ne baki ɗaya, mai cigaba da tafiyarsa da aikinsa.

Yaƙin Tabuk:

Yaƙin Tabuk na cikin muhimman abubuwan da suka faru a tarihin Musulunci a watan Ramadan

Annabi SAW ya tura Imam Ali a matsayin jagoran rundunar yaƙi zuwa Yemen.

Mutane da dama ne suka Musulunta kuma suka ƙara yawan rundunar Musulmai.