
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban taron jam’iyyar ADC da aka shirya ya shiga halin rashin tabbas sa’o’i gabanin fara gudanarwa, bayan waɗansu zarge-zarge da jam’iyyar ta yi akan cewa akwai yunƙurin hana ta amfani da wurin taron da ta karɓa duk da cewa ta ƙulla yarjejeniya da mai shi da kuma biyan cikakken kuɗin da aka buƙata.
A wata sanarwa da aka aike wa manema labarai, ADC ta zargi mai wurin da fuskantar matsin lamba na ya janye yarjejeniyar da ya ƙulla da jam’iyyar don haddasa tsaiko ga taron.
A cewar jam’iyyar, hukumar gudanarwar Rainbow Event Centre ta sanar da ita cewa Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCDA) da Ministan Abuja Nyesom Wike na matsa musu akan bayar da wajen ga ADC.
Haka kuma, jam’iyyar ta yi zargin cewa an yi wa mai wajen barazanar karɓe masa lasisinsa na aiki matuƙar ya bari aka yi taron a wajen nasa.
Saidai duk da wannan batu, ADC ta tirje akan lallai za ta gudanar da taron nata kamar yadda aka tsara saboda tana ƙullalliyar yarjejeniyar da mai wajen taron.
