
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin Paparoma Leo na 14 ya yi watsi da rahotannin da ke cewa yana rikici da Shugaba Donald Trump na Amurka, inda ya ce ba shi ra’ayin yin takun saƙa da jagorann Amurkan.
“Ni ba ɗan siyasa ba ne. Ba ni da niyyar yin muhawara da shi”, inji Paparoma.
Ya bayyana cewa, “Saƙon duk ɗaya ne: don yaɗa zaman lafiya”, kamar yadda ya bayyana wa manema labarai.
Jagoran addinin ya faɗi haka ne yayin da ya cilla zuwa Aljeriya a ziyararsa a Afirka karon farko a matsayin shugaba.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Trump ya ya caccake shi akan kalamansa game da yaƙin da Amurka ke yi da Iran.
