‘Yan sanda sun kama mutane 188 bisa zargin aikata laifuka daban-daban a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta sanar da kama mutane 188 bisa zargin aikata laifuka da suka shafi ta’addanci,fyaɗe da dallancin miyagun ƙwayoyi a jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar a katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana haka a bayanin da yake wa manema labarai kan nasarorin da suka samu a cikin watan da ya wuce.

Ya ce rundunar ‘yan sandan sun kama mutanen da aikata laifuka daban daban har guda 120 a faɗin jihar.

DSP Sadiq Aliyu ya bayyana cewa laifuka 98 na gaban kotu da suka haɗa da laifuffukan fashi da makami guda 14 da na fyaɗe guda 20.

Sauran sun haɗa da zargin dillancin miyagun ƙwayoyi guda 22 da laifin satar dabbobi da kuma masu ba yan bindiga bayanan sirri su biyar yace.

Haka kuma DSP Sadiq ya bayyana cewa yan sanda duk a watan da ya wuce sun samu nasarar kama wani da ake zargi da kisan wani mutum mai suna ‘Abu Amshi’ a cikin garin Katsina wanda yanzu haka yan sanda na bincike kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da shi a gaban kuliya.

Ya ce yan sanda sun ƙubutar da mutane 21 da yan bindiga suka yi ƙoƙarin garkuwa da su tare da gano bindigogi bakwai.

Bindigan sun haɗa da ,PKT guda biyu da AK 47 su ma guda biyu da bindiga kirar gida guda uku tare da albarusai guda 974 masu rai.

‘Yan sandan sun kuma ƙwato dabbobi guda 30 da ɓarayin dabbobi suka sace da baburan hawa na yan bindiga guda biyar.

DSP Abubakar Sadiq ya ce kwamishinan yan sanda Ali Umar Fage ya yabawa jami’an sa bisa namijin ƙoƙarin da nuna ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan su da ya kai su ga nasara.

CP Fage ya tabbatarwa al’ummar jihar da cewa haɗin gwiwa na jami’an tsaro a jihar suna nan ba dare ba rana domin ganin sun kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.

By ukarofi