Taron Ibadan: Jam’iyyun adawa sun zaɓi fitar da ɗan takara ɗaya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɓangaren adawa a siyasar Nijeriya na shirin ɗaukar wani salo yayin da a ranar Asabar haɗakar ‘ya’yan jam’iyyu suka cimma matsayar ajiye bambance-bambancen da ke tsakanin da tsayar da ɗan takara ɗaya da zai ƙalubalanci jam’iyya mai mulki (APC) a babban zaɓen 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa, wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da dan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 na jam’iyyar LP, Peter Obi da wasu manyan ‘yan siyasa na goyon bayan ra’ayin kafa gamayyar jam’iyyun adawa a Nijeriya.

Ana ganin wannan mataki a matsayin yunƙurin kauce wa rarrabuwar ƙuri’a ’u, wadda a baya ta kan raunana jam’iyyun adawa a zaɓukan ƙasa, wanda haɗuwa a kan dan takara ɗaya tilo zai taimaka wajen ƙarfafa ɓangaren adawa.

Jam’iyyun da suka haɗu a taron, wanda aka yi a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, sun haɗa da: Peoples Democratic Party (PDP), African Democratic Congress (ADC), Peoples Redemption Party (PRP), New Nigeria Peoples Party (NNPP), National Democratic Coalition (NDC), Labour Party (LP), Action Peoples Party (APP), Accord Party, Allied Peoples Movement (APM), Action Alliance (AA), Democratic Labour Party (DLA), Young Progressives Party (YPP), Action Democratic Party (ADP) da kuma Zenith Labour Party (ZLP) da dai sauransu.

Wannan gamayya na da burin ƙarfafa dimukraɗiyya a Nijeriya, inganta gasa a siyasa, da kuma daƙile abin da wasu ke kira karkata zuwa tsarin jam’iyya daya mai ƙarfi, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Zuwa yanzu dai ba a yanke hukunci akan wanda zai zama dan takara da zai wakilci gamayyar ba, amma ana sa ran cigaba da tattaunawa kafin lokacin babban zaɓen.

By Babaji