Atiku, Obi, Kwankwaso, Makinde da wasu sun haɗu Ibadan yayin babban taron ‘yan adawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu manyan ‘yan siyasar adawa sun isa birnin Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, domin halartar wani muhimmin taron ‘yan adawa da ake sa ran zai tattauna batutuwan siyasa da yiwuwar haɗin kai gabanin zaɓen 2027.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya tabbatar da zuwansa ta hanyar wallafa saƙo a shafukansa na sada zumunta da kuma nuna bidiyon da ke bayyana saukarsa a Filin Jiragen Sama na Ibadan a ranar Asabar. A cikin sakon, an ga Atiku cikin annashuwa tare da magoya bayansa da suka tarbe shi.

Haka kuma, tsohon Gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, yana daga cikin waɗanda suka isa wurin domin halartar tattaunawar matakin koli da za a gudanar.

Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya tabbatar da isowarsa tun safiyar Asabar, inda ya wallafa hotuna a shafinsa na Facebook tare da bayyana shirinsa na shiga tattaunawar.

Sauran manyan mahalarta sun haɗa da tsohon Sakataren Ƙasa na APC, Ishola Akpanudoedehe, da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar.

Akan haka ne aka tsaurara tsaro a wajen taron yayin da ake ci gaba da isowar manyan baƙi, tare da taruwar magoya bayan bangarorin siyasa daban-daban domin jiran sakamakon tattaunawar.

By Babaji