Tsohon ɗan wasan gaba na Super Eagles ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar Super Eagles ta Nijeriya, Michael Eneramo, ya rasu sakamakon bugun zuciya yayin wani wasan sada zumunta a Jihar Kaduna.

Hukumar Ƙwallon Kafa ta Ƙasa NFF, ta ce Eneramo mai shekaru 40 ya gamu da bugun zuciya ne mintuna biyar bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a wasan, lamarin da ya tilasta tsayar da wasan domin duba halin da yake ciki.

Duk da cewa, an yi yunƙurin ba shi agajin gaggawa a filin wasan da kuma gaggauta garzayawa da shi zuwa asibiti, hakan bai sa ya samu tsira ba.

Babban Sakataren NFF, Mohammed Sanusi, ya bayyana al’amarin a matsayin abin tashin hankali, inda ya miƙa ta’aziyya ga iyalai da abokan arziƙin marigayin da kuma daukacin al’ummar ƙwallon ƙafa bisa wannan rashi.

Marigayi Eneramo ya taka rawar gani a tarihin ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, inda ya wakilci ƙasar a wasanni da dama, kuma aka san shi da ƙarfi da jajircewa a filin wasa, abin da ya sa ake masa laƙabi da “The Tank” a lokacin da yake taka leda a ƙungiyoyin ƙasashen waje daban-daban.

Rasuwarsa ta girgiza masoya ƙwallon ƙafa da ‘yan wasa a sassa daban-daban na duniya musamman ganin yadda ya bayar da gagarumar gudunmawa a fannin.

By Babaji