
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Dakta Muttaqha Rabe Darma a matsayin sabon ministan gidaje da ci-gaban birane daga Jihar Katsina, bayan Majalisar Dattawa ta tantance shi.
Ya maye gurbin Ahmed Musa Ɗangiwa, wanda ya yi murabus kwanan nan daga muƙamin.
Shugaban, a taron wanda aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa, ya taya Dakta Darma murna bisa zuwa kan muƙamin a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubale wajen ci-gaban ƙasa.
Tinubu ya shaida masa cewa ya shirya sauke nauyin da aka ɗora masa bisa jajircewa da ƙwarewa kamar yadda ya nuna a baya yayin da yake riƙe da wasu muƙaman gwamnati.
Dakta Darma ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Bayero da ke Kano a fannin Injiniyancin Ƙere-ƙere, sannan daga bisani ya yi na biyu a Injiniyancin Samarwa daga Jami’ar Benin.
Haka kuma ya yi karatu na digirin digirgir a fannin Gudanar da Kasuwanci a Jami’ar Liverpool ta ƙasar Ingila da kuma digiri na uku a Injiniyancin Masana’antu a Jami’ar Atlantic International da ke Amurka.
Kazalika, ya bayar da gudumuwa a fannin ilimi, inda ya yi aikin lakcaranci a Jami’ar Bayero ta Kano.
Gabanin naɗa shi, shi ne Shugaban Cibiyar Ci-gaban Al’umma ta Umar Musa Yar’Adua a Katsina.
