
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon ɗaya daga cikin amintattu na ƙasa na Ƙungiyar Ma’aikatan Fetur da Gas ta Ƙasa (NUPENG), Salimon Oladiti, ya zama sabon shugaban ƙungiyar.
A ranar Juma’a ne aka zaɓi Olditi a muƙamin a yayin babban taron ƙungiyar karo na 6 da aka yi Legas.
Haka kuma, an naɗa tsohon Shugaban reshen samar da Mai da Gas, Akin Oladejo a matsayin mataimakin shugaba.
