Tattalin arziƙin Nijeriya na fuskanta barazana sakamakon yaƙin Isra’ila da Iran – CPPE

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Cibiyar Bunƙasa Kasuwancin Al’umma (CPPE) a ranar Lahadi ta ce, yaƙin da ake tsakanin Iran da Isra’ila yana barazana da ta fuskoki masu yawa ga tattalin arziƙin Nijeriya.

Wannan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da daraktan cibiyar, Muda Yusuf, ya sanya wa hannu wanda ya ce ɓarkewar yaƙin tamkar ƙara wa Borno dawaki ne ƙarin matsalolin ga tattalin arzikin duniya.

“Ga tattalin arziƙin Nijeriya tasirin na da yawa. Akwai barazana mai yawa ga tattalin arziƙin ƙasar nan,” inji Yusuf.

A ranar Juma’a da safe ne kasar Isra’ila ta harba wa Iran makami mai linzami wacce ta ba da hujjar cewa manufar harin shi ne hana Iran ɗin mallakar makamin ƙare dangi da aka fi sani da Nukiliya. Sai dak ƙasashe da yawa na kallon hakan da abin da bai dace ba saboda Iran na kan tattaunawa da ƙasar Amurka. Kuma ita Iran ta ce tana sarrafa makamin ne da niyya mai kyau ta zaman lafiya da samun makamashi.

A cikin jawabin na ranar Lahadi, Yusuf ya ce, idan aka cigaba da wannan rikici, Nijeriya za ta fuskanci ƙarancin samun kuɗin shiga da zuba jari a ɓangaren mai da iskar gas.

Ya kuma ce babban ma’aunin na tattalin arzikin Nijeriya shi ne farashin mai a duniya.

Sannan ya ce tashin farashin mai a duniya zai shafi kuɗin da Nijeriya ke samu daga ƙasashen waje saboda mai ne babbar hanyar da take samun kuɗin waje da shi.

“Farashin ɗanyen mai zai karu zuwa Dala 75% wanda ƙarin ya kai kaso 15% kafin ɓarkewar rikicin Isra’ila-Iran. Wannan zai shafi kudaɗen asusun Nijeriya na ajiya a ƙasashen waje. Kuma abin da zai samar da daidaiton al’amura shi ne yadda farashin kuɗin kasashen wajen zai kasance idan aka kwatanta da Naira,” ya faɗa.

A cewarsa, bangaren man fetur shi ke kawo wa Nijeriya kaso 50% na kuɗin shigarta.

Sai dai ya ce ta wata fuskar abin zai shafi masu zuba jari, domin idan yaƙin ya cigaba da faruwa, da yiwuwar a samu karin kuɗin shiga.

”ƙarin farashin mai labari ne mai faɗi ga masu zuba jari a mai da iskar gas,” ya bayyana.

Yusuf ya ce, yaƙin kasashen Isra’ila da Iran ya tada farashin ɗanyen mai daga Dala 65 zuwa Dala 75 a cikin satin da ya gabata. Wannan karin da aka samu ya kai kaso 15% a ciki ‘yan kwanaki kaɗan.

“Wannan tabbas yana da tasa illar ga harkar mai a duniya.”

A cewarsa, tattalin arziki ƙasashen duniya ciki har da Nijeriya za su samu ƙarin kuɗin da suke kashewa wajen sayen fetur da dizal da man jirgin sama da gas da sauran kayayyaki dangin mai.

“Wannan abu zai shafi tattalin arziki da kasuwanci masu yawan gaske,” ya faɗa.

Ya kuma kara da cewa, tsadar makamashi babban ma’auni ne na hauhawar farashin kaya a Nijeriya.

“Tasirin kuɗin samar da kayayyaki da na sufuri da da samar da makamashi zai haifar da hauhawar kayayyaki. Kuma dukkan wannan lissafi ne da zai shafi mai sayen kaya na can ƙasa kuma ya danganta da yadda al’umma suka nisanci amfani da wasu kayayyakin.”

Yusuf ya ce, hauhawar farashi na shafar kuɗin ruwa saboda yadda mahukunta ke la’akari da shi wajen kallon tsadar kayayyaki.

Ya ce akwai bukatar ɓullo da tsare-tsare na tafi da kuɗi a Nijeriya saboda tashin farashin makamashi da na kuɗin ruwa dukkansu ma’auni ne da za su shafi ribar kasuwanci na tattalin arzikinmu” ya faɗa.

Sannan ya ce, masu zuba hannun jari na da bai danganci man fetur ba su ne za su fi jin jiki.

“Abin zai fi shafar kamfanin kasuwanci da suke da alaƙa da Gabas ta Tsakiya da su samun kayayyaki daga yankin saboda rashin kwanciyar hankali a yankin.”

“Don haka Nijeriya za ta iya samun kuɗin shiga mai yawa daga bangarori man saboda ƙaruwar buƙatar man fetur a duniya.”

By ukarofi