
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗariƙar Tijjaniya a Nijeriya, ta koka game da cigaba da tsarewa da gurfanar da ɗaya daga cikin jagororinta, Sheikh Abdulƙadir Sani Khalifa Zariya, inda ta bayyana hakan a matsayin takura da kira da a bi umarnin doka.
A wata takarda da ta aike wa manema labarai a yau Litinin da ke ɗauke da sanya hannun Sheikh Ibrahim Shehu Maihula, wato Mataimakin Shugaban Majalisar Shura ta Tijjaniya, ɗariƙar ta ce ta shiga halin tilas ne na yin magana akan al’amarin musamman ganin yadda aka cigaba da tsare shehin malamin, wanda ya shafe tsawon kusan watanni biyar a komar hukuma ba tare da gurfanarwa a kotu ba.
Tijjaniya, wadda ke da mabiya kusan miliyan 60 a Nijeriya da sauran sassan Afirka ta Yamma, ta jaddada ƙoƙarinta na tabbatar da zaman lafiya, adalci da biyayya ga doka, tana mai cewa malamin mutum ne da ake girmamawa bisa karantarwarsa na addini da zamantakewa.
An tsare malamin ne tun a ranar 11 ga Disambar 2025 a lokacin da ya je hedikwatar bankin Ja’iz da ke Abuja domin warware matsalar takunkumin da aka sanya wa asusun bankinsa.
A nan ne jami’an hukumar leƙen asiri (DIA) suka kama shi bisa zargin sa da hannu a haddasa yaƙi a Nijeriya da aikata wasu ayyukan ta’addanci.
Daga bisani, Babbar Kotun Tarayya a wata shari’a da Alƙali Peter Lifu ya jagoranta, ta umarci a gaggauta sakin malamin tare da ayyana takunkumin da aka sanya wa asusun nasa a matsayin abin da aka yi ba bisa doka ba.
Haka kuma, ta umarci a biya shi diyyar Naira miliyan 6 na dameji, bisa abin da ta kira da tauye masa ‘yanci.
