Tinubu ne ya yanke shawarar cire tallafin fetur, ba mu muka sa shi ba – IMF

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Kuɗi ta Ƙasa-da-ƙasa (IMF), ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya so cire tallafin man fetur a Nijeriya, ba wai su suka ba shi shawara ba.

Daraktan Shiyyar Afirka na hukumar, Abebe Selassie ya bayyana hakan a ranar Juma’a, a yayin zaman IMF da Bankin Duniya da ke gudana a birnin Washington DC dake Amurka.

Ya ce, aikinsu ya taƙaitu ne a tattauanawa akai-akai da ƙasashe, kamar yadda suka yi da Japan da Ingila.

A ranar farko da Shugaba Tinubu ke shiga ofishi a shekarar 2023, ya sanar da cewa ya cire tallafin fetur wanda ya yi sanadiyyar tashin farashin litarsa daga wajen N200 har ya kai zuwa N1,200 a sassa da dama a ƙasar.

Watanni kaɗan bayan haka ne Naira ta shiga halin rugujewa a kasuwannin duniya wanda hakan ya sabbaba tsananin tsadar rayuwa acikin al’umma wadda har yanzu ake cigaba da fama da ita.

Yayin da ake tsaka da haka ne Shugaba Tinubu ya yi ta kira ga al’umma da su kasance masu haƙuri, ya mai cewa ba zai sauya matsaya ba game da hukuncin nasa.

Shugaban ƙasar ya na da fahimtar cewa gyare-gyaren da ya ke yi a ɓangarori daban-daban, ababe ne da zasu amfani al’umma na tsawon lokaci sakamakon tsare-tsare da ya samar don ci-gaban ƙasar.

By Babaji