Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Nijeriya daga taron Abu Dhabi ADSW da babbar yarjejeniya mai darajar dala biliyan 30, wadda ke nuni da wani muhimmin mataki na ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar nan ta fannin jarin raya muhalli wato ‘Green Finance’ da sauyin makamashi.
A cewar wata sanarwa da Mai bai wa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, Nijeriya ta ƙulla wata muhimmiyar yarjejeniya ta tattalin arziki da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) wadda aka sani da ‘Comprehensive Economic Partnership Agreement’ (CEPA).
Yarjejeniyar an sanya hannu ne a gefen taron, inda aka bayyana cewa za ta ƙara bunƙasa haɗin gwiwa a fannonin kasuwanci, zuba jari, musayar fasaha da kuma manyan sassa kamar makamashi, ababen more rayuwa, noma da ma’adinai.
Shugaba Tinubu ya ce wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen jawo sabbin jarin ƙasashen waje tare da ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin Nijeriya da UAE.
Ya kuma sanar da cewa za a gudanar da taron INVESTOPIA na haɗin gwiwar Nijeriya da UAE a birnin Legas a watan Fabrairu, wanda ake sa ran zai zamo dandali na jawo manyan masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.
A jawabinsa a taron, Shugaban ƙasar ya bayyana aniyar Nijeriya na tattara dala biliyan 30 a duk shekara domin tallafa wa harkokin sauyin makamashi da masana’antu masu kula da muhalli. Ya ce ƙasar na ƙoƙarin hanzarta sauya tsarin samar da wutar lantarki tare da lantarki zuwa sassan ƙasar baki ɗaya.
Tinubu ya jaddada cewa Nijeriya na da ɗimbin damar sauyin yanayi da ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba, musamman a fannonin tattalin arziki, lafiya, makamashi da samar da abinci.
Ya ce, idan aka yi amfani da waɗannan damar yadda ya dace, za su amfanar da Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.
Shugaban ƙasar ya halarci taron ne bisa gayyatar Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan. A taron, Tinubu ya kuma yi nuni da cewa Nijeriya na da tsayayyen tsarin kula da kasuwar carbon, bayan amincewa da National Carbon Market Activation Policy (NCMAP) da kuma kafa National Carbon Registry, wanda ke taimakawa wajen inganta tsarin rahoton hayaƙi da tabbatar da sahihancinsa.
Masana na ganin wannan yarjejeniya a matsayin wata babbar dama ga Nijeriya wajen jawo sabbin jarin ƙasashen waje da ƙarfafa ƙoƙarin ƙasar na yaƙi da sauyin yanayi, tare da bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa.
