Tinubu ya amince da sabbin jerin sunayen waɗanda aka yi wa afuwa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sabbin jerin sunayen mutanen da za su amfana da shirin afuwa na gwamnatin tarayya da kuma shirin afuwa na Shugaban ƙasa, inda Maryam Sanda wacce aka yanke wa hukuncin kisa ba ta a cikin jerin sunayen.

An sanar da hakan ne a ranar Laraba ta hanyar wata sanarwa da Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara Kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, inda ya tabbatar da cewa amincewar ta biyo bayan nazari mai zurfi da tattaunawa da Majalisar Zartarwa bisa ga Sashe na 175 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara).

A cewar sanarwar, sabon matakin an yi shi ne don daidaita adalci da tausayi, tare da kare tsaron ƙasa da kuma haƙƙoƙin waɗanda abin ya shafa.

Fadar Shugaban ƙasa ta fayyace cewa an cire waɗanda aka samu da laifuka masu tsanani – ciki har da sace mutane, safarar mutane, laifukan miyagun ƙwayoyi, zamba, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba daga cikin jerin waɗanda aka yi wa afuwar.

Daga cikin waɗanda aka yi wa afuwa ta shugaban ƙasa a ƙarƙashin Dokar Shugaban ƙasa ta Afuwa (Grant of Pardon) 2025 akwai: Mrs. Anastasia Daniel Nwaobia, Barr. Hussaini Alhaji Umar, Ayinla Saadu Alanamu, Hon. Farouk M. Lawan, Herbert Macaulay, Manjo-Janar Mamman Jiya ɓatsa, da Ken Saro-Wiwa, tare da wasu da ke da alaƙa da shari’ar Ogoni Nine – Asabar Dobee, Nordu Eawo, Daniel Gbako, Paul Leɓera, Feliɗ Nuale, Baribor Bera, Barinem Kiobel, da John Kpuine.

Bugu da ƙari, an mayr da hukuncin ɗaurin rai da rai ga wasu mutane huɗu da aka yanke wa hukuncin kisa – Emmanuel Baba, Abubakar Usman, Khalifa Umar, da Mohammed Umar – a ƙarƙashin Dokar Shugaban ƙasa ta Jinƙai (Customation of Death Jumping to Life In prison) ta 2025.

Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana aikin afuwa a matsayin wani ɓangare na ci gaba da alƙawarin Shugaba Tinubu na gyaran shari’a da kuma tsarin adalci na shari’a.

“Shugaba Tinubu yana godiya da ra’ayoyin jama’a da masu ruwa da tsaki kuma ya sake nanata alƙawarin gwamnatinsa na tabbatar da adalci yayin da yake rage shi da tausayi,” inji sanarwar.

By ukarofi