Tinubu ya amince da tallafin Naira biliyan biyu ga waɗanda harin Filato ya shafa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da bayar da Naira biliyan 2 a matsayin tallafin agaji ga waɗanda harin da aka kai a ranar 29 ga Maris a Angwan Rukuba, Jos, ya shafa, yayin da ya buƙaci shugabanni da masu ruwa da tsaki su rungumi zaman lafiya domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke yawan faruwa a jihar Filato.

Ministan harkokin jinƙai, Mohammed Dorro, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani zama na tattaunawa da aka gudanar a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, wanda ya ɗauki tsawon sa’o’i uku.

Taron ya samu halartar wakilai 32 daga jihar Filato ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Caleb Mutfwang, ciki har da tsoffin gwamnoni na jihar.

A yayin taron, Shugaba Tinubu ya ƙalubalanci mahalarta taron da su duba tsoffin rahotannin “White Paper” na gwamnati kan rikice-rikicen tsaro, tare da dawo da shawarwari masu amfani da za a iya aiwatarwa domin kawo mafita mai ɗorewa.

Ya kuma buƙaci shugabanni da su kasance jakadu na haƙuri da zaman lafiya, tare da kira ga gwamnan jihar da ya gano tare da fallasa waɗanda ke haddasa rikice-rikice domin a hukunta su bisa doka.

Tinubu ya ce, “Ba wani tsari ko shamaki a nan — mun taru ne domin mu faɗi gaskiya tare da nemo mafita ta dindindin ga rikice-rikicen da ke maimaituwa.”

Ya ƙara da cewa dole ne shugabanni su dakatar da ɗaukar mutane domin tayar da rikicin ƙabilanci da kashe-kashe a tsakanin al’umma.

Wannan taro ya cika alkawarin da shugaban ƙasar ya yi a lokacin da ya ziyarci jihar Filato bayan harin Angwan Rukuba, inda ya yi alƙawarin haɗa manyan masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro a jihar.

Masu jawabi a taron sun bayyana cewa rikicin “asali da baƙi” (indigeneship), addini, ƙabilanci da kuma rikicin manoma da makiyaya ne manyan abubuwan da ke haddasa rikice-rikicen a jihar.

Wakilan matasa Musulmi da Kirista sun yi alƙawarin yin aiki tare domin samar da zaman lafiya da kuma bai wa gwamnan jihar cikakken goyon baya.

Sarkin Jos, Gbong Gwom Jos, Da Jacob Gyang Buba, ya buƙaci shugaban ƙasa da ya ƙara yawan jami’an tsaro a jihar, ya samar da na’urorin CCTV, tare da hanzarta dawo da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu kafin damina ta fara.

A nasa ɓangaren, gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da dukkan tsoffin gwamnoni na jihar suka taru wuri guda domin tattauna batun tsaro, yana mai alƙawarin ci gaba da gina kan wannan yunƙuri domin sauya rikici zuwa damar bunƙasa tattalin arziki ga al’ummar jihar.

By ukarofi