Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayar da umarni da a gaggauta kammala aikin titin Nnamdi Azikiwe, domin daƙile yawaitar haɗurra da ke haddasa asarar rayuka.
Umarnin ya biyo bayan wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki suka gudanar bisa umarnin Gwamna Uba Sani, wanda ya nuna matuƙar damuwarsa kan karuwar haɗɗura a kan titin mai tsawon kilomita 21.5.
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana damuwar gwamnan tare da jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa.
Ya ce, “Gwamna ya nuna matuƙar damuwa kan asarar rayukan da ake yi a wannan hanya. Babu wani ci gaba da zai iya zama hujjar rasa ko da rai guda. Wannan lamari ba za a iya jurewa ba, dole ne a ɗauki mataki nan take.”
Taron ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki ciki har da wakilan Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta ƙasa (FRSC), Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kaduna (KASTELEA), da kuma kamfanin Dangote da kamfanin gina titin Dantata & Sawoe. Haka kuma shugabannin ƙungiyoyin sufuri kamar NARTO, NURTW da ACCOMORAN sun halarta.
Maiyaki ya bayyana cewa duk da cewa an bayar da kwangilar aikin tun a shekarar 2021 kafin zuwan wannan gwamnati, aikin ya yi tafiyar hawainiya har sai da Gwamna Uba Sani ya shiga tsakani.
“Tun bayan sa hannun gwamna kai tsaye, an samu ci gaba mai kyau. Amma hakan kaɗai bai isa ba, yanzu dai kammala aikin cikin lokaci ya zama wajibi,” inji shi.
Rahotanni daga jami’an kula da hanyoyi na tarayya da kuma masu aikin sun nuna cewa an kammala kusan kilomita 19 na titin. Duk da cewa an tsara kammala aikin a watan Disambar 2026, gwamnan ya buƙaci a kawo ƙarshen aikin kafin lokacin.
“Gwamna ya bayyana ƙarara cewa dole ne a kammala aikin kafin wa’adin da aka tsara. Ba za a amince da wani jinkiri ba.”
Domin tabbatar da bin wannan umarni, gwamnatin ta kafa wani kwamitin haɗin gwiwa na hukumomi da zai riƙa sa ido kan aikin tare da tabbatar da tsaron hanya, musamman a lokacin damina.
Kwamitin, wanda Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ke jagoranta, ya haɗa da FRSC, KASTELEA, jami’an Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, masu kwangila, wakilan al’umma, sarakuna da ƙungiyoyin sufuri. Haka kuma, an ɗora wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai alhakin wayar da kan jama’a domin sauya halayen amfani da hanya.
Maiyaki ya jaddada cewa halayen masu amfani da hanya na daga cikin manyan dalilan haɗɗura, inda aka gano wurare masu haɗari da ke buƙatar kulawa ta musamman.
“Baya ga ingancin titi, halayen mutane na da matuƙar tasiri. Muna aiki tare da al’umma domin tabbatar da bin ƙa’idojin hanya. Dole ne a kawo ƙarshen tuƙin ganganci.”
Ya kuma ƙara da cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa aikin ya dace da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa, ba kawai wajen gina titi ba, har ma da yadda ake amfani da shi.
Wannan mataki na gwamnati ya biyo bayan matsin lamba daga shugabannin al’umma da ƙungiyoyin matasa, waɗanda suka bayyana halin da ake ciki a matsayin matsalar tsaro mai tsanani da ke da illa ga tattalin arziki da zamantakewa.
Gwamnatin jihar ta ce, da sabbin matakan da aka ɗauka, tana da ƙudurin dawo da tsaro, gaggauta kammala aikin, da kuma tabbatar da cewa titin Western Bypass ya cika manufarsa ba tare da ƙara asarar rayuka ba.
