Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani mutum mai shekaru 60 tare da ƙona wasu kadarori a yayin wani hari da suka kai ƙauyen Gidan Wando da ke ƙaramar H toukumar Bakori a jihar Katsina.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:06 na yammacin ranar Talata, lokacin da maharan, waɗanda suka zo kan babura kimanin guda 17, suka mamaye ƙauyen tare da buɗe wuta kan al’umma.
Rahotanni sun nuna cewa haɗaɗɗiyar tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da kuma ‘yan sa-kai sun gaggauta kai ɗauki, inda suka fafata da maharan a wani artabu da ya tilasta musu tserewa, lamarin da ya dawo da zaman lafiya a yankin.
A yayin harin, wata harsashi da ta kauce hanya ta sami wani mutum mai suna Sabiu Mohammed, wanda aka bayyana a matsayin ɗan kasuwa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
Haka kuma, gobara ta tashi a shagon sayar da kayan amfanin gona na mamacin, wadda daga bisani ta bazu zuwa wasu dakuna guda biyu da ke kusa.
Daga baya jami’an tsaro tare da mazauna yankin sun yi nasarar kashe gobarar tare da hana ta yaɗuwa.
An garzaya da mamacin zuwa asibiti domin ba shi kulawa, sai dai likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
A halin yanzu, jami’an tsaro sun ƙara tsaurara sintiri a yankin, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin cafke maharan da suka tse
