Daga SULAIMAN HUSSAINI, D/Kudu
Kakakin jam’iyyar APC a jihar Kano, Kwamaret Auwalu Soja Sani Mai Nagge, ya bayyana cewa jihar Kano ba ta taɓa samun gwamnan da ya yi mata aiki kamar Gwamna Abba Kabir Yusuf ba.
Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Kano, inda ya ce ko tsofaffin gwamnoni da ake yabawa ba su kai irin ayyukan da gwamnan na yanzu ya yi cikin ƙanƙanin lokaci ba.
Ya ce daga cikin ayyukan da aka gudanar akwai inganta hanyoyi, gyaran makarantu da asibitoci, samar da kayan aiki na zamani, tallafawa matasa da mata da jari, da kuma magance matsalar ruwa.
Haka kuma ya ce gwamnan ya samar da ayyukan yi ga matasa tare da inganta ma’aikatu domin bunƙasa tattalin arziki.
Auwalu Soja ya ƙara da cewa wannan ci gaba ya sa jam’iyyar APC ke ƙara samun karɓuwa a wajen al’umma, yana mai hasashen nasara a zaɓe mai zuwa.
Ya kuma yi kira ga waɗanda ba su shiga jam’iyyar ba da su gaggauta shigowa domin samun ci gaba mai ɗorewa.
