Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban hukumar tallafa wa masu neman bashi ta ƙasa (NCGC), Yakubu Dogara, ya ce, Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya gaji matsalar tattalin arziƙi ne a lokacin da ya kama mulki a watan Mayun 2023 wanda shi ne dalilin da ya tilasta masa ƙaddamar da sauye-sauye domin guje rugujewar ƙasar nan.
Dogara ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja a lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin taron ƙaddamar da lakca kan ‘yan majalisa da aka yi wa take da: “Fahimtar sauye-sauyen haraji a Nijeriya: ƙarin haske game da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu.”
Ya bayyana sabon dokar sake fasalin haraji da shugaba Tinubu ya sa wa hannu a watan Yunin 2025 da kasancewa “gyara mai cike da jarumta da nufin sauya tarihin Nijeriya.”
Dogara wanda tsohon shugaban majalisar wakilai ne, ya ce, a lokacin da Tinubu ya karɓi mulki daga tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, tattalin arziƙin Nijeriya ya gama taɓarɓarewa.
Ya kuma ce an buga tsabar kuɗi har na Naira tiriliyan 22.7 da aka sa a cikin tattalin arziƙin Nijeriya ta hanyar wani tsari mai cike da fargaba wanda hakan ya jawo karyewar darajar Naira a hannun mutane.
Ya kuma ce, “kawo zuwa lokacin da Tinubu ya karɓi mulki, ɓurɓushin tattalin arziƙin Nijeriya ne ya ragu wanda hakan a bayyane yake. An buga Naira tiriliyan 22.7 da zuba ta cikin tattalin arziƙin Nijeriya ta wani tsari mai wanda ya lalata kuɗin da ke hannun mutane.”
Ya kuma nuna cewa batun tsarin musayar kuɗin waje, ya bai wa wasu mutane damar samun ɗaruruwan miliyoyin kuɗi ta hanyar babban bankin Nijeriya (CBN) da ke ba su wannan kuɗin musayar ba tare da suna samar da kowanne irin kaya ko nau’i na hidimta wa al’umma ba.
Dogara ya kuma nuna cewa wannan ta’ada ta sayar da man fetur wajen karɓar bashi ta hanyar lamuni, abu ne da ya zama ruwan dare a gwamnatin da ta gabata.
“Wasu daga cikin bashin ƙasashen waje an karɓe su ne da nufin ƙarfafa darajar Naira, wannan tsari ne marar kan kado.”
A lokacin da wannan matsala ke fukanto shi, a cewar Dogara, Tinubu ba shi da wani lokaci da zai kashe na jin daɗi.
“Daga rana ta farko, ya fahimci akwai buƙatar ɗaukar mataki na gaggawa domin hana tattalin arziƙin Nijeriya rugujewa,” ya faɗa.
Ya kuma bayyana Tinubu da cewa shi mai kawo gyara ne wanda ya fahimci tsarin dimokradiyya ya bai ‘yan siyasa ‘yanci da kuma amfani da tsarin tafi da tattalin arziki da zai kasance bisa adalci musamman ga mutane masu rauni domin farfaɗo da su daga halin kaɗuwa da suke ciki.
Domin magance matsalar tsohon tsarin tattara haraji a Nijeriya a cewar tsohon ɗan majalisar, shugaba Tinubu ya kafa kwamitin duba sha’anin kuɗi da sake fasalin haraji.
Ya bayyana shawarar kwamitin da na juyin juya hali, da ke ƙoƙarin ƙoƙarin raba Nijeriya da da tsohon tsari da faɗaɗa tsarin karɓar haraji da sauƙaƙa hanyar biyan haraji da dawo da Nijeriya kan tsarin karɓar haraji na duniya.
Hangen nesa da kwamitin ya nuna ya nuna shi ne na kare talaka da ƙarfafa wa kasuwanni da ƙarfafa zuba hannun jari da samar da daidaito da ƙarfafa ƙwazo.
Harajin da shugaban ƙsa ya sanya wa hannu a ranar 26 ga watan Juni (NTA), 2025, dokar haraji ta ƙasa (NTAA), 2025, dokar samar da hukumar karɓar haraji (NRSA), 2025, da hukumar karɓar haraji ta haɗin guiwa (JRBA), 2025.
Waɗannan dokokin karɓar haraji, a cewar Dogaro ya ce, za su cure waɗannan tsofaffin hanyoyin karɓar haraji guda 4 da aka samar.
A game da harajin kaso 5% na man fetur da ke cikin sabuwar dokar haraji, Dogara ya yi bayanin cewa wannan doka ba sabuwa ba ce, domin akwai dokar a cikin dokar hukumar kare haɗura ta shekarar 2007 (da aka yi wa gyara).
Ya jaddada cewa ba zai shafi makamashin da al’umma ke amfani da shi a gida kamar kananzir da iskar gas na LPG da CNG da makamashi sabuntau.
Ya kuma jaddada cewa wannan haraji ba zai fara aiki ba a watan Janairun 2026 ba kamar yadda ministan kuɗi.
Tsohon kakakin majalisar ya ce dokar haraji ya gamu da tutsu daga waɗanda suke cin moriyar tsohon tsarin.
“A wasu lokuta waɗanda suke ƙin wannan dokoki suna yi ne saboda ba sa kishin ganin tattalin arziƙin Nijeriya ya inganta, burinsu shi ne shugaban ƙasa ya gaza.”
Duk da yaba wa sauye-sauyen da aka yi, Dogara ya ce akwai wasu ƙalubale muhimman da suka haɗa da rashin yin bayanin game da sabuwar dokar da akwai giɓi a ɓangaren fasaha da abin da ya shafi laifuka na intanet da rashin ƙwarewa kula da sabon tsarin da ƙaruwar kuɗin da za a kashe wajen sanya al’umma su bi wannan sabon tsari.
Sai dai ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su tallafa wa shugaba Tinubu domin tabbatar da an aiwatar da dokokin da ɗorewarsa.
Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kalli kansu a matsayin masu ruwa da tsaki a wani ɓangare na gina tattalin arziƙi mai ɗorewa da ƙasa mai yin gogayya da takwarorinta na duniya.
