Tallafin kayan haihuwa ya kai ga mata masu ciki 400 a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Ƙaramar hukumar Gombe ta raba kayayyakin haihuwa kyauta ga mata masu juna biyu 400, a wani shiri na musamman da aka ƙaddamar domin inganta lafiyar uwa da jariri tare da rage mace-macen da ke faruwa a lokacin haihuwa.

An gudanar da bikin rabon ne a cibiyar haihuwa ta Gombe, inda shugaban ƙaramar hukumar, Barista Sani Ahmad Haruna (Wakilin Arewan Gombe), ya jagoranci ƙaddamarwar.

A jawabin sa, Haruna ya bayyana cewa shirin ya yi daidai da umarnin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ƙarfafa kiwon lafiya a matakin farko, musamman wajen kula da mata masu juna biyu da ƙananan yara.

Ya ƙara da cewa, nan gaba za a fara gwajin jini kyauta ga mata masu ciki a dukkan cibiyoyin haihuwa na ƙaramar hukumar, domin gano matsalolin lafiya da wuri kafin su tsananta.

Wasu daga cikin mata da suka amfana sun bayyana farin cikinsu tare da gode wa gwamnati bisa tallafin da suka ce zai rage musu nauyin kuɗin kula da haihuwa da kuma kare lafiyar su da na jariran da za su haifa.

By ukarofi