
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya gayyaci Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, tare da manyan jagororin tsaro zuwa Abuja sakamakon sabon harin kisan gilla da ya auku Unguwar Rukuba da ke garin Jos.
Za a yi zaman ne domin yin nazari akan halin tsaro da ɗaukar matakan da suak dace wajen kare sake aukuwar irin haka a nan gaba.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa taron na da nufin tsara ingantaccen mataki na haɗin gwiwa domin magance rikicin tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankula tare da cigaba da kiyaye doka da oda yayin hukumomi da gwamnati ke ƙoƙarin shawo kan al’amuran da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar al’umma.
Tuni dai jami’an tsaro ƙarƙashin “Operation Enduring Peace’ suka fara bazuwa a yankin, inda ake ƙarfafa sintiri da kuma gudanar da ayyuka na musamman domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin.
