Ministan Lantarki, Adelabu ya musanta yin murabus daga muƙamin

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ya musanta rahotannin da ke cewa ya ajiya muƙaminsa na minista, yana mai bayyana su a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a yayin da ake raɗaɗi akan goben siyasarsa.

Hakan na zuwa ne a daidai da Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarni ga masu riƙa da muƙamai acikinta da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027 da su ajiye muƙamin da akabasu.

Da yake tsokaci akan al’amarin a wata hirar WhatsApp da manema labarai a jiya Talata, mai taimaka wa Adelabu akan harkokin yaɗa labarai, Bolaji Tunji, ya yi watsi da rahotannin waɗanda ya kira a matsayin ƙarya, yana mai cewa ministan yana nan daram a muƙamin nasa na riƙe fannin lantarkin Nijeriya.

Haka kuma ya ƙaryata hotunan da ke yaɗawa da suke ƙarfafa batun murabus ɗin.

Duk da cewa an yi hira da shi a ranar inda har aka tambaye shi akan makomarsa a siyasa, sai ya amsa da cewa har yanzu yana kan muƙaminsa kuma zai cigaba da aiki tuƙuru wajen sauke nauyinsa.

A cewarsa, magance matsalolin da ke fannin ke fuskanta a Nijeriya shi ne muradinsa.

By Babaji