Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masarautu ta Jihar Katsina (MLGEA) ta gudanar da sa ido kan yadda aka rarraba magungunan da aka samar domin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) a faɗin jihar.
An gudanar da wannan aiki ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar, Hon. Bishir Tanimu Dutsinma, tare da mai ba gwamna shawara kan ayyukan ƙananan hukumomi, Hon. Lawal Rufa’i Safana, da sauran manyan jami’an ma’aikatar, domin duba yadda aka miƙa magungunan, hanyoyin rabawa, yanayin ajiyarsu da kuma yadda aka rubuta bayanansu a ƙananan hukumomi.
Masu sa ido a yankunan Katsina, Funtua da Daura sun tabbatar da cewa an gudanar da komai yadda ya kamata, an adana magungunan a wuri mai kyau, kuma an kiyaye dukkan bayanan ajiyar su.
Haka kuma, an umarci ma’aikata da su tabbatar da an rarraba magungunan cikin gaggawa da gaskiya ga PHCs masu amfani, a gaban shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.
Ma’aikatar ta yaba wa jami’an ƙananan hukumomi bisa bin ƙa’idoji da kuma yadda suka gudanar da aikin rarraba magungunan cikin nasara a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar.
