
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An sake shiga fargaba a wasu sassan Jihar Filato yayin da wani sabon rikicin ya ɓarke, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Rikicin na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da gwamnatin jihar ta ɗage dokar ta-ɓaci ta sa’o’i 48 da aka kafa tun da fari, biyo bayan wani hari da wasu mahara sanye da kayan soja suka kai wa al’ummar yankin Rukuba a ranar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan unguwar Unguwar Rukuba da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa sun riƙa kai wa juna farmaki a yau Laraba.
Shaidu sun ce, rikicin ya samo asali ne da safiyar yau a yankin makarantar firamare ta UNA a lokacin da wasu matasa ɗauke da sanduna, adduna, da wasu makamai suka fara kai wa mutane farmaki.
Wannan al’amari ya yi al’amari ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da munanan raunuka.
Mazauna yankin sun caccaki gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang, inda suka bayyana cewa an sassauta dokar ta-ɓacin daga ƙarfe 7 na safe zuwa 3 na yamma da wuri ba tare da samar da wadataccen tsaro a yankin ba.
