Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
’Yan wasan ƙwallon ƙafa bakwai daga Kwalejin Ƙwallon Kafa ta Jihar Katsina (Katsina Football Academy) sun bar Najeriya zuwa ƙasar Portugal domin halartar babbar gasar neman ƙwarewa ta IBER Estoril Lisbon 2026.
’Yan wasan da suka tafi sun haɗa da Muhammad Hussain, Mannir Abdullahi, Ibrahim Abdu Haro, Nura S. Nura, Muhammad Muktar Katuka, Isah Usman Ali, da Abubakar Anas.
Sun tashi ne daga filin jirgin sama na Murtala Muhammed zuwa birnin Lisbon da fatan samun damar zama ƙwararrun ’yan wasa a ƙasashen waje.
Hakan ya biyo bayan haɗin gwiwar da Kwalejin ,ta ƙulla da Moonluck FA Lagos domin bai wa matasa masu baiwa damar cika burinsu na zama ƙwararrun ’yan kwallon kafa.
Kwamishinan Wasanni na Jihar Katsina, Engr. Surajo Yazid Abukur, tare da daraktan wasanni na Moonluck FA, Datti Yusuf Umar, ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwar domin bunƙasa harkar matasa.
Gasanr da za a ɗauki kwanki biyar ana fafatawa,manyan ƙungiyoyin Turai da suka haɗa da AS Roma, Manchester City, Juventus, FC Porto, Benfica da Blackburn Rovers za su halarta.
Daraktan Kwalejin, Shamsuddeen Ibrahim, ya yi wa ’yan wasan bankwana tare da jan hankalinsu su zama jakadu nagari na jihar Katsina, inda ya kuma yabawa Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa kan goyon bayan da yake bayarwa ga cigaban kwalejin.
