Tinubu ya jinina wa Shettima kan hidimar ƙasa yayin zagayowar ranar haihuwarsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya taya Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima bisa cikar sa shekaru 60 a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin abokin aiki mai daraja kuma mai kishin ƙasa kan hidima, jajircewa da sadaukarwa don ƙasa da al’ummarta.

Tinubu, a wani saƙon zagayowar ranar haihuwarsa na cikar Shettima shekara 60 a ranar 2 ga Satumba, 2026, ya taya matar Mataimakin Shugaban Ƙasar Hajiya Nana, ‘ya’yansa, iyalai da abokan siyasa bisa wannan muhimmin lokaci.

Tun a ranar 1 ga Satumba, 2026 ne aka fitar da sanarwar mai ɗauke da sanya hannun Tinubu, Shugaba kuma Kwamandan Rundunonin Tsaron Tarayyar Jamhuriyar Nijeriya. Tinubu ya taya Shettima murna, wanda ya bayyana a matsayin “ɗan uwana kuma abokin aiki wajen jagorantar ƙasarmu” wajen kaiwa shekara 60.

Ya bayyana cewa, Shettima ba kaɗai amintaccen na hannun dama ko abokin aiki mai daraja ba ne, mutum ne mai kishin ƙasa wajen hidima, jajircewa da sadaukarwa a gare ta.

Shugaban har wa yau, ya ce a yayin taya Shettima murna, Nijeriya ma tana yaba wa aikinsa na ma’aikacin banki da kuma tarihinsa abin koyi ga Jihar Borno da ma ƙasar baki ɗaya, yana mai cewa ba a iya ƙidaya jajircewarsa kan ci-gaba da haɗin kan ƙasa.

Kazalika, ya yaba wa ƙoƙarinsa musamman kan biyayya ga jam’iyyar APC, goyon bayansa ga gwamnatin da kuma sadaukarwa wajen cimma nasarori a ajandar Sabunta Fata ta shugaban ƙasa da dai sauransu. A ƙarshe, Tinubu ya yi masa godiya kan ƙoƙarin sauke nauye-nauyen alƙawuran da suka ɗauka na Sabunta Fata ga ‘yan Nijeriya tare da addu’ar Allah ya cigaba da ba shi kariya da ƙarfafa masa gwiwar hidimta wa al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply