Tinubu ya kashe Dala miliyan 801 a sayen makaman Amurka cikin wata 18 – IMPI

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Independent Media and Policy Initiative (IMPI) ta bayyana cewa, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sayi makaman yaƙi daga Amurka da darajar su ta kai dala miliyan 801 (kimanin naira tiriliyan 1.15) cikin watanni 18 kacal da suka gabata, a wani ɓangare na shirin sabunta kayan tsaron ƙasa.

A cikin wata sanarwa da Shugaban ƙungiyar, Dr. Omoniyi Akinsiju, ya sanya wa hannu, IMPI ta bayyana cewa wannan jarin ya nuna yadda gwamnatin Tinubu ke da jajircewa wajen ƙarfafa tsaro da inganta ƙarfin sojojin Nijeriya.

Akinsiju ya ce shekarar 2024 ta kasance mafi yawan kashe kuɗin makamai da Nijeriya ta taɓa yi a ‘yan shekarun nan, inda aka kashe fiye da naira biliyan 520, wanda ya kai kusan kashi 67% na dukkan kuɗaɗen da aka kashe wajen sayen makamai daga 2020 zuwa 2024.

Ya bayyana cewa cikin manyan cinikin da aka ƙulla akwai sayen jirgin mai saukar ungulu 12 nau’in AH-1Z Viper daga kamfanin Bell Teɗtron na Amurka da darajar ta kai dala miliyan 455, domin ƙarfafa aikin yaƙar ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga.

Haka kuma, a watan Agustan 2025, Nijeriya ta rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta dala miliyan 346, domin sayen bama-bamai 1,000 na MK-82 da kayan harba makamai 5,000 na APKWS, tare da kayan horo da na tallafin aiki.

A cewar IMPI, wannan matakin zai taimaka wajen ƙara inganta fasahar kai farmaki da daidaito (precision-strike) da kuma shirin sojojin ƙasar wajen tunkarar Boko Haram, ISWAP da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.

Akinsiju ya ƙara da cewa, “Wannan irin jarin makamai na nuna ƙarfin gwiwar Tinubu wajen yaƙar ta’addanci da kare rayukan ‘yan Nijeriya. Rahotannin baya-bayan nan daga Amurka kan Nijeriya na iya zama wani bangare na fafatawar kasuwancin makamai tsakaninta da China, fiye da damuwa kan addini ko haƙƙin bil’adama.”

By ukarofi