Tinubu ya sa hannu kan dokar kafa Hukumar Raya Arewa ta Tsakiya

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan ƙudirin dokar kafa Hukumar Raya Yankin Arewa ta tsakiya (NCDC), wanda hakan ke nufin dokar ta zama doka mai aiki a ƙasar.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a ranar Talata. Ya ce kafa wannan hukuma zai taimaka wajen kawo ci gaba ga yankin, musamman a matakin karkara. Akpabio ya kuma taya al’ummar yankin Arewa ta tsakiya murna, yana mai fatan dokar za ta kawo ci gaba da zaman lafiya a yankin.

Wannan lamari na ci gaba da haifar da martani daga ɓangarori daban-daban, inda ake sa ran ƙarin bayani nan gaba.

By ukarofi