
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wani yunƙuri na bunƙasa masna’antun cikin gida, Shugaba Bola Tinubu ya amince da dokar hana fitar da ƙwallon kaɗanya da ake sarrafawa wajen samar da man-kaɗai har na tsawon watanni shida.
Umurnin, wanda zai fara aiki nan take ya biyo bayan rahotannin tafka asara da Nijeriya ke yi sakamakon ficewa da ɗanyar kaɗanyar kafin sarrafawa, lamarin da daƙile kasuwanci da ƙarfafar masana’antun cikin gida.
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, wanda ya sanar da dakatarwar a yayin wani taron masu ruwa da tsaki, ya bayyana cewa matakin zai ƙara darajta kasuwancin man-kaɗai ta hanyar farfaɗo da masana’antun sarrafa kayan gida, ta yadda za su samar da ayyukan yi da ƙarin kudaden shiga ga mazauna karkara musamman mata.
Shettima ya yi hasashen cewa sake tsara kasuwancin kaɗanya zai taimaka wajen samar da ribar kusan dala miliyan 300 a duk shekara.
Duk da cewa Nijeriya ce kan gaba wajen noman kadanya a duniya, a halin yanzu bata mallakin fiye da kashi 1% daga ribar dala biliyan 6.5 da Kwallon ke samarwa a kasuwannin duniya.
A cewar Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, an ƙiyasta cewa Nijeriya na asarar kimanin tan dubu 90 na ɗanyen man kaɗanya a duk shekara sakamakon rashin bin ƙa’idojin cinikayya na bai-ɗaya.
Ana sa ran matakin da zai biyo bayan dakatarwar zai taka rawa waken rage dogaron da Nijeriya ke yi da man fetur wajen samar da kuɗaɗen shiga.
Tuni ƙasashe masu maƙwabtaka da Najeriya da suka hada da Ghana, Burkina Faso, Mali, da Togo suka ɗauki irin mataki don farfaɗo da kasuwancin ƙwallon kaɗanya a ƙasashensu.




