Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Kimiyya ta Azare zuwa Sheikh Ɗahiru Bauchi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare a Jihar Bauchi zuwa Jami’ar Sheikh Usman Ɗahiru Bauchi.

Tinubu ya sanar da hakan ne a yau Asabar, a lokacin da ya isar da ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin a garin Bauchi.

A cewar Shugaban Ƙasar, matakin ya sami ne domin karrama kyawawan ayyukan da marigayin shehin malamin ya bari na karantarwa a tsawon rayuwarsa da ya shafe kusan ƙarni guda.

Lamarin da ya taimaka wa ci-gaban al’umma a Nijeriya da ma ƙasashen waje.

Haka kuma, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin wanda ya rayu bisa horo da son zaman lafiya acikin al’umma, wanda ya sa aka samu ɗimbin mabiyansa da ke ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiyar ƙasa.

Kazalika, Tinubu ya ce hakan da ya yi ɓangare ne na yaba wa ƙoƙarin ƴan mazan jiya daga Gwamnatin Tarayya, waɗanda sun bada gagarumar gudumawa wajen inganta rayukan al’ummar ƙasa.

By Babaji