
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya ce, babu wanda zai yi yunƙurin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 sai ‘ɗan ta-kife ko ɗan basaja’ da an san ba zai kai labari ba.
Shettima ya bayyana haka ne a taron Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar APC karo na 15 a babban ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A cewarsa, ba a cin zaɓe ta kafar Soshiyal Mediya ko kuma kafafe irin su Twitter wanda a yanzu ya zama X, inda za a yi ta kumfar baki wajen kururuta abin da ba haka yake ba a zahirin gaske.
Ya ce, ana cin zaɓe ne ta ƙirga ƙuri’ar da jama’a suka kaɗa yayin da suka zaɓi ƴan takarar da suka cancanta, ba da yaɗa surutu ko wani shiririta ba.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa, bisa la’akari da ƙwarewar mai gidan nasa, an samu darussa a baya da a yanzu har zuwa 2027 za su taimaka wajen yin nasara yayin da jama’ar ƙasa suka fito domin kaɗa ƙuri’a.
