Tinubu ya umarci a rage adadin wakilan Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin duniya

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A wani yunƙuri na rage adadin kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci a rage adadin wakilai da Nijeriya ta saba turawa zuwa taron majalisar ɗinkin duniya karo na 79 da za a yi a birnin New York da ke Amurka a watan Satumba.

Sanarwar ta fito ne daga ofishin shugaban ma’aikatan Fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila a ranar Asabar a wani taron kwana ɗaya da hukumar gudanarwa ta offishin ta yi.

Hakan na zuwa ne bayan da mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwar cewa kaɗai waɗanda aka tabbatar da su ne za su halarci taron.

Gbajabiamila ya yi bayani game da tsadar harkar shugabanci, ya na mai bada misali da adadin wakilan Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin duniya inda ya ce, a baya wasu na amfani da damar taron wajen yin harkokinsu da ba su shafi gwamnati ba.

Ya ƙara da cewa, shugaba Tinubu ya bayyana cewa a wannan shekarar, matuƙar mutum bai da wani nauyi da ya rataya akan sa a taron, to kar ya je Amurka.

Shugaban ma’aikatan, ya kuma yi ƙarin haske game da hukuncin, ya na mai bayyana hakan a matsayin wata hanya ta rage tsadar gudanar da harkokin gwamnati da kuma inganta su.

By Babaji