Tinubu zai ƙaddamar da manyan ayyuka a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai kawo ziyarar aiki na kwanaki biyu a Jihar Katsina inda zai ƙaddamar da manyan ayyuka guda biyu da gwamnatin jihar ta ƙaddamar a jihar.

Da yake hira da manema labarai a gidan gwamnatin jihar, Kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya bayyana cewa Tinubu zai ƙaddamar da hanyar rantse da ta taso daga Katsina zuwa hanyar Dutsinma ta zarce zuwa hanyar Kano.

Ya ƙara da cewa shugaban ƙasan zai ƙaddamar da cibiyar haɗe haɗe na kayan aikin noma na zamani a jihar.

Kayayyakin sun haɗa da injinan motocin taraktoci da wasu kayan amfanin noma da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta sayo daga Sin wato hina. Inji kwamishinan.

Haka kuma ziyarar shugaban ƙasa da zai kawo jihar zai ba gwamnatin jihar damar zama da shugaban ƙasar domin maka ƙorafe-ƙorafe da suka haɗa da matsalar tsaro a jihar. Dr Bala ya ce.

Sai yayi kira ga al’ummar Jihar Katsina da su fito su yi ma babban baƙo maraba.

By ukarofi