Tinubu zai gana da shugaban Chana kan tattalin arziƙi a Beijing

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya shirya haɗuwa da shugaban ƙasar Jamhuriyar Chana a birnin Beijing wanda za a yi a satin farko na watan Satumba, kamar yadda mai magana da yawunsa, Cif Ajuri Ngelale ya faɗa.

Za a yi ganawar ne kan batun muhimman ababen harkar tattali da suka haɗa ƙasashen biyu inda za a shirya takardar yarjejeniya wanda aciki akwai; ‘green economy’ da ‘blue economy’ da kuma shirye-shiryen Ƙasa.

Kawo yanzu ba a faɗi takamaiman ranar da Shugaba Tinubu zai bar Nijeriya ba.

Cif Ajuri ya ce Shugaba Tinubu zai tattauna kan manyan batutuwa da shugaban na Chana tare da shugabannin manyan kamfanoni don alaƙar tattali da ke tsakanin su.

Haka kuma, tattaunawar za ta ƙunshi batutuwan ƙasa, shiyya da kuma tsaro na ƙasa-da-ƙasa wanda za a mayar da hankali kan kammala tashar jirgin ƙasa na Legas-Kaduna ta ɓangaren Abuja-Ibadan.

Bugu da ƙari, akwai batutuwan salo na fasahar sadarwa, tace mai da gas da kuma sauran nau’ukan fasaha.

By Babaji