Tinubu zai iya gyara tattalin arzikin Nijeriya kuma ya yaƙi rashawa – Shettima

Spread the love

Mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta dimokuradiyya ta hanyar gyara matsalolin tattalin arziki, tabbatar da tsaron al’umma, yaƙi da cin hanci da rashawa, ƙarfafa ɓangaren shari’a, da kuma inganta haɗin kan ƙasa. Shettima, wanda mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a taron ƙasa kan dimokuraɗiyya da Cibiyar Jagoranci da Dabaru ta Afrika (ACLSD) ta shirya a Abuja.

A jawabinsa, ya bayyana cewa koda yake dimokuraɗiyya ba cikakkiyar hanya ce ba, ita ce mafi alkhairi idan aka kwatanta da sauran tsare-tsare na mulki. Ya ce gwamnatin yanzu tana sane da matsalolin da ‘yan ƙasa ke fuskanta tare da himmatuwar magance su. Shettima ya ƙara da cewa ana ɗaukar matakai masu kyau don ganin an samu ci gaba tare da rage raɗaɗin da ‘yan ƙasa ke ji, yana mai kiran jama’a da su bayar da gudunmawarsu wajen cimma burin ƙasa.

Haka zalika, tsohon mataimakin shugaban ƙasar Ghana, Dr. Mahamudu Bawumia, wanda ya gabatar da jawabin karshe, ya bayyana cewa duk da nakasun da ke tattare da dimokuradiyya, ita ce kaɗai hanya mafi kyau da za ta bai wa ‘yan ƙasa ‘yanci da haƙƙoƙi. Ya bayyana cewa don dimokuraɗiyya ta samu cigaba, dole ne a samu ingantattun cibiyoyi da suka dace da kare haƙƙin jama’a da taƙaita amfani da ƙarfin mulki ba tare da izini ba.

A nasa ɓangaren, tsohon mataimakin shugaba ƙasa Atiku Abubakar ya nuna damuwa game da halin da dimokuraɗiyyar ke ciki a ƙasar, yana mai cewa tana fuskantar barazana daga ɓangarori daban-daban. Ya ce akwai buƙatar shugabanni su zama masu biyayya ga dokoki da al’umma, tare da tabbatar da cewa tsarin mulki yana amfani wa duk ‘yan ƙasa ba tare da nuna banbanci ba.

By ukarofi