Daga UMAR GARBA a Katsina
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar aiki ta kwana biyu zuwa Jihar Katsina.
Bayanin haka na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, da yammacin ranar Alhamis a shafinsa na sada zumunta.
Onanuga ya ce shugaba Tinubu zai fara ziyarar ranar Juma’a, shugaban zai gana da masu ruwa da tsaki domin nazartar yanayin tsaro a jihar.
Sanarwar ta ce shugaban zai ƙaddamar da cibiyar ayyukan noma ta zamani da wani titi mai hannu biyu, mai tsawon kilomita 24 da gwamnan jihar Dikko Raɗɗa ya kammala.
Haka kuma Bayo Onanuga ya ce Shugaba Tinubu zai kuma halarci ɗaurin auren ƴargidan gwamnan jihar ta Katsinan kafin kammala ziyarar tasa.
