
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis ne Shugaba Bola Tinubu zai sanya hannu la sabon ƙudirin dokar haraji da aka yi wa garambawul guda huɗu, lamarin da zai sauya fasali da tsarin kuɗaɗen haraji a Nijeriya.
Ƙudirorin harajin sun haɗa da ƙudirin haraji na Ƙasa da ƙudirin tattara haraji na Ƙasa da samar da na hukumar kuɗaɗen haraji da kuma na samar da hukumar haɗaka ta haraji, waɗanda suka tsallake karatu a Majalisar Dokoki ta Ƙasa biyo bayan nazari mai zurfi da shawartar masu-ruwa-da-tsaki.
A yayin da aka ƙaddamar da sababbin tsarin harajin, ana sa ran za su taimaka wajen sauya tsarin tattara haraji a Nijeriya, lamarin da zai sa samu ƙarin kuɗaɗen shiga da bunƙasa zuba jari a ciki da wajen Nijeriya.
Haka kuma, a yayin ƙaddamarwar a Fadar Shugaban Ƙasa, za a samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai, Shugaban mafiya rinjaye na majalisun da sauran su.
Sai kuma Shugaban ƙungiyar gwamnoni, Ministan Tattali da na Kuɗi da kuma Antoni Janar na Ƙasa.
