Gwamnatin Amurka ƙarƙashin shugabancin Donald Trump ta sanar da sabbin haraji masu tsanani da suka kai har 50% kan kayayyakin da Indiya ke shigarwa kasuwannin Amurka. Wannan mataki, a cewar Trump, na da nufin hukunta New Delhi saboda ci gaba da sayen mai mai arha daga Rasha.
Amurka ta ce sayen man Rasha na nufin tallafa wa yaƙin da Moscow ke yi a Ukraine. Indiya dai ta sayi fiye da kashi ɗaya bisa uku na danyen man fetur nata daga Rasha a bara.
Masana sun yi gargaɗin cewa wannan sabon haraji zai iya lalata kasuwancin Indiya da Amurka, wacce ita ce babbar kasuwar fitar da kayayyaki ta Delhi, inda ta sayi kaya sama da dala biliyan 87 a shekarar 2024.
ƙididdiga ta nuna cewa sama da dala biliyan 48 na kayayyakin fitar Indiya ne wannan sabon haraji zai shafa, ciki har da masana’antar tufafi, sassaƙaƙƙen duwatsu da kayan ado, kifi, fata da ƙananan motoci. Masana tattalin arziki sun ce wannan zai jawo asarar ayyukan yi musamman ga ƙananan masana’antu masu dogaro da ma’aikata masu yawa.
Sai dai wasu muhimman fannoni kamar magunguna da na’urorin lantarki an keɓe su daga wannan mataki na farko, amma akwai yiwuwar su ma a saka su a gaba. Firayim Minista Narendra Modi ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta miƙa wuya ga matsin lambar Amurka ba, musamman kan harkar noma da kiwo.
