Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Darurruwan ‘yan Nijeriya ne ke ci gaba da zama gudajen yarin ƙasar Habasha a cikin mawuyacin hali yayin da yarjejeniyar fahimtar juna ta diplomasiyya da aka daɗe ana jira tsakanin ƙasashen biyu na fuskantar tsaiko.
Yayin da yake magana a ranar Laraba, ƙaramar Ministan Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta tabbatar da cewa Nijeriya ta kammala dukkan ƙa’idojin da suka dace amma ta zargi Habasha da yin jinkiri wajen aiwatarwa.
“Ma’aikatar ta cika nata ɓangaren na ƙa’idojin miƙa waɗanda aka yanke wa hukunci. ɓangaren Habasha ne ke jinkiri,” inji ta a wata sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin yaɗa labarai, Magnus Eze ya fitar.
Alƙaluman ma’aikatar sun nuna cewa, sama da ‘yan Nijeriya 270 ne ke zaman gidan yari a ƙasar Habasha, waɗanda akasarinsu bisa laifukan da suka shafi muggan ƙwayoyi ne.
ƙungiyoyin fararen hula da iyalan fursunonin na ci gaba da nuna damuwa game da yadda ake cin zarafi da rashin kula da gidajen yarin Habasha.
Ambasada Onwuka Collins, shugaban gidauniyar My Dreamalive Development Foundation, ya bayyana yanayin da ke cikin kurkukun Habasha a matsayin abin takaici, yana mai gargaɗin cewa ana asarar rayuka saboda rashin kulawa.
“Abin baƙin ciki ne cewa tuni wasu ‘yan Nijeriya da ke gidan yarin Habasha suka mutu sakamakon waɗannan munanan yanayi, yayin da wasu ke fama da cututtuka da suka haɗa da ciwon ƙoda da shanyewar ɓangaren jiki.
Collins ya ce, “Ba za mu iya ci gaba da kallon yadda ’yan uwanmu suke cikin kurkuku ba tare da shari’a ta gaskiya ba. Saboda haka, muna buƙatar taimakon gaggawa.”
Ya yi zargin cewa fursunonin suna jure rashin isassun abinci, ko kaɗan ko rashin kulawar lafiya, sakaci, muguwar ɗabi’a, da karɓar kuɗi daga jami’an gidan yari.
A watan Nuwamba 2024, wata babbar kotun tarayya a Nijeriya ta umurci ma’aikatar harkokin wajen ƙasar da hukumar ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje (NiDCOM) da su gaggauta dawo da ‘yan ƙasar da ake tsare da su a ƙasar Habasha.
Kotun ta kuma lura da shigar Habasha cewa ba ta da isassun tanadin kasafin kuɗi don kula da fursunonin ƙasashen waje.
Duk da hukuncin da aka yanke, ba a samu ci gaba konkaɗan ba, lamarin da ya jefa fursunoni da dama da iyalansu cikin ɗimuwa.
A ranar 17 ga Afrilu, 2025, Ambasada Odumegwu-Ojukwu ya jagoranci tawagar Nujeriya don ganawa da Jakadan Habasha a Najeriya, Legesse Geremew Haile, a Abuja. Ta matsa wa Habasha lamba da ta gaggauta amincewa da yarjejeniyar, inda ta bayyana takaicin jinkirin da aka samu.
“Mutanenmu ba sa son jin cewa wani fursuna ɗan Nijeriya ya mutu a gidan yarin Habasha,” inji ta.
A martanin da ya mayar, Ambasada Haile ya sake tabbatar da ƙawancen Habasha da Nijeriya amma ya amince har yanzu yarjejeniyar tana jiran amincewar Majalisar Wakilan Habasha, wanda ya tsawaita zaman.
Sakamakon jinkirin ya kasance yana haifar da asarar rayuka. A ranar 12 ga Maris, 2023, wani fursuna dan Najeriya mai suna Favor Eze, ya mutu a gidan yarin Kaliti da ke Addis Ababa bayan da jami’ai suka yi masa wulaƙanci.
Wani fursuna, Uchenna Nwanneneme, ya mutu a ranar 21 ga Satumba, 2023, sakamakon cutar tarin fuka, bisa zargin rashin kulawar da ta dace.
Yayin da iyalai ke jira cikin ɓacin rai, makomar ‘yan Nijeriya sama da 270 da ke maƙale a gidajen yarin Habasha ya rataya a wuyan siyasar Habasha na kammala yarjejeniyar miƙa su.
