Tsananin zafi ya yi sanadin mutuwar mutane 50,000 a Turai

Spread the love

Aƙalla mutane 47,000 ne suka mutu saboda matsanancin zafi a nahiyar Turai a shekarar 2023, a yayin da lamarin ya fi tsananta a ƙasashen da ke kudancin yankin, kamar yadda Cibiyar Bibiyar Harkokin Kiwon Lafiya ta Duniya, wato Bacelona Institude for Global Health ta wallafa a ranar Litinin ɗin nan.

Bayanan mujallar Cibiyar ta Barcelona Institude for Global Health sun nuna cewa tsanantar zafin da aka fuskanta a shekarar da ta gabata, ya zarta na dukkanin lokutan da suka gabata da aka sani.

Cibiyar ta ci gaba da cewa a yayin da sauyin yanayi ke ci gaba da haifar da tsananin yanayin zafi, yankunan Turai na cikin halin ha’ula’i, a yayin da al’ummar yankin da dama ke fuskantar ƙalubale na cututtuka mabambanta a sanadiyar zafin.

Yayin da sauyin yanayi ke ci gaba da ƙara ta’azzara zafi, al’umar da ke yankin Turai na rayuwa ne a cikin mawuyacin hali a nahiyar da ke fuskantar ɗumamar yanayi sama da ko’ina a duniya, inda suke fuskantar barazanar rashin lafiya a sanadin tsananin zafi.

Masu bincike sun yi amfani da bayanan mace-macen da aka samu a sanadiyar yanayin zafi daga ƙasashen Turai 35, inda aka yi ƙiyasin cewa mutane 47,690 ne suka mutu a sanadiyar wasu dalilai da ke da alaƙa da tsananin zafin.

A yayin da matsalar ta fi ƙamari a ƙasashe irinsu Girka da Bulgaria da Italiya da kuma Spain waɗanda suka fi samun adadi mafi yawa na mace-mace masu alaƙa da zafin

By ukarofi