Tsoffin ‘yan majalisa na fuskantar matsanancin talauci bayan barin majalisa – Sanata Na’Allah

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Sanata Bala Ibn Na’Allah ya yi wani hoton rayuwa da ba a taɓa ganin irinsa ba bayan siyasa, inda ya bayyana cewa wasu tsofaffin ‘yan majalisar dokoki a Nijeriya da wuya suke iya biyan buƙatunsu na yau da kullum, inda wasu da dama ke ta faman biyan kuɗin makarantar ‘ya’yansu.

Da yake magana a cikin shirin minti 30 na Trust Teleɓision, tsohon Sanatan Kebbi ta Kudu ya ƙalubalanci aƙidar da mutane ke yi na cewa riƙe muƙaman gwamnati na tabbatar da dukiya.

“Ku je kowace mazaɓa ko kuma inda kuka san inda tsoffin ‘yan majalisar suke zama,” inji Na’Allah ga mai gabatar da shirin, Mannir Dan-Ali. “A nemo Sanata ɗaya ko ɗan Majalisar Wakilai da ba shi da wata sana’a ko sana’a kafin siyasa, a duba ko za su iya biyan kuɗin makarantar ‘ya’yansu bayan shekara ɗaya kawai.”

Na’Allah ya ƙara da cewa kyakykyawan hoton rayuwa da ‘yan Nijeriya ke dangantawa da ‘yan majalisar bai nuna ainihin abin da ke faruwa a majalisar dokokin ƙasar ba. 

Ya ce da yawa sun shiga siyasa suna tunanin za a samu riba ta kuɗi, sai dai su fuskanci takaici da wahala daga baya.

“Wasu mutane suna shiga Majalisar Dokoki ta ƙasa suna tunanin wuri ne na samun kuɗi, amma sun fi talauci,” inji shi.

Lokacin da mai gabatar da shirin ya nuna cewa da yawa daga cikin tsofaffin ‘yan majalisar sun yi kyau, sai Na’Allah ya amsa da cewa, “Haka ake gani daga waje, ina roƙon ku da ku je ku bincika, ku dawo ku yaɗa rahoton da kuka samu.

Tsohon Sanatan, wanda ya taɓa zama mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ta 8, ya fayyace cewa ba wai yana kare ‘yan siyasa ba ne, amma yana son ya gyara ra’ayoyin jama’a game da dukiya da muƙamin siyasa.

Ya ƙara da cewa da yawa daga cikin ‘yan majalisu suna zaman su ne ba don wata riba ba, sai dai don fatan samun muƙamai masu girma.

“Sun ci gaba, suna fatan wata rana za su iya zama Shugaban Majalisar Dattawa ko wani abu mafi ƙarfi – ba wai kawai su ci gaba da zama sanatoci na yau da kullum ba.”

By ukarofi