
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kamfanin shirya wasan dambe na WWE ya tabbatar da rasuwar fitaccen ɗan wasan kokawa Hulk Hogan.
Hogan, wanda asalin sunansa Terry Bollea, na ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan kokawa a shekarun 1980 da 1990, kuma ya shahara a wasu fannonin nishaɗantarwa daban-daban.
Hogan, wanda ya shafe shekaru 71 a duniya, ya rasu ne bayan samun ɗaukewar bugun zuciya a gidansa dake birnin Clearwater.
Ganin haka ya sa aka garzaya da shi wani asibiti a safiyar ranar Alhamis, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Hakan ya faru ne makonnin kandan da matar Terry Bollea ta yi watsi a jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya yi dogon suma, kamar yadda TMZ ta ruwaito.
