Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani tsohon jami’in Rundunar Sojin Nijeriya, Manjo Toye Akinlade (mai ritaya), ya shigar da ƙara a gaban Kotun Kwadago ta ƙasa (NICN) da ke Abuja, yana zargin rundunar sojin da wasu manyan jami’anta da cin zarafin iko, sake tura shi aiki ba bisa ƙa’ida ba, da kuma tilasta masa ci gaba da aikin soja duk da ya riga ya ajiye takardar murabus.
Rahotanni sun nuna cewa ƙarar, mai lamba NICN/ABJ/379/2025, Akinlade na neman kotu ta ayyana cewa murabus ɗinsa daga Rundunar Sojin Nijeriya ya fara aiki nan take bayan hukumomin da suka dace sun karɓi wasiƙar, kuma duk wata umarni, ladabtarwa ko iko da aka ci gaba da yi masa bayan hakan ba ta da tushe a doka, kuma ta saba wa Kundin Tsarin Mulki.
Waɗanda ake ƙara sun haɗa da Rundunar Sojin Nijeriya, Kanal Samson O. Okebukola da Kanal D.O. Ehicheoya.
A cikin takardun shari’a da aka gabatar, Akinlade ya bayyana cewa ya miƙa wasiƙar murabus ɗinsa mai kwanan wata 11 ga Nuwamba, 2025, zuwa ga Babban Hafsan Sojin ƙasa da sauran hukumomin da abin ya shafa. Sai dai ya yi zargin cewa duk da an karɓi wasiƙar, rundunar ta ci gaba da ɗaukarsa a matsayin jami’i mai aiki.
Ya shaida wa kotu cewa an sake tura shi aiki ba tare da amincewarsa ba, an ba shi tambayoyi da ladabtarwa ba tare da bin ƙa’ida ba, duk bayan murabus ɗinsa ya riga ya fara aiki. Daga cikin buƙatunsa, yana rokon kotu ta tantance ko murabus ɗinsa ya inganta da zarar an karɓe shi, da kuma ko waɗanda ake ƙara suna da hurumin ladabtar da shi bayan hakan.
Tsohon Manjon ya kuma kalubalanci wata tambaya da aka ba shi a ranar 12 ga Disamba, 2025, wadda ya ce an fitar da ita ne bisa umarnin ɗaya daga cikin waɗanda ake kara bayan ya riga ya fice daga aikin soja. A cewarsa, wannan tambaya ba ta da inganci a doka, domin an bayar da ita ne bayan an raba shi da aikin.
Haka kuma, Akinlade ya soki wata wasiƙar nuna rashin jin daɗi da aka aike masa, wadda ta kunshi hukuncin tsawatawa da gargaɗi. Ya ce an dauki matakin ladabtarwar ba tare da kafa Kwamitin Bincike ko Kwamitin Tantance Laifi ba, abin da ya saɓa wa ƙa’idojin soja da aka tanada.
A cikin rantsuwar da ya yi wa kotu, Akinlade ya bayyana cewa bayan ya nuna adawa da matakan ladabtarwar, an sake tura shi daga Jos zuwa Basawa a Zariya a matsayin hukunci, matakin da ya ce ya saɓa wa dokokin gudanarwa na rundunar. A kalamansa, “saboda gajiya da wuce gona da iri da cin zarafin iko daga ɓangaren jami’i na biyu ba tare da tsawatarwa daga manya ba, sai na mika takardar murabus.”
Ya ƙara da cewa, duk da murabus ɗinsa, ana ci gaba da umartar sa ya je aiki a Zariya tare da ɗaukarsa a matsayin jami’i mai aiki. Haka kuma, ya zargi rundunar da hana shi hutun jinya bayan ya faɗi yana aiki, inda aka kwantar da shi a asibiti. A cewarsa, gwaje-gwajen likita sun nuna cewa hawan jininsa na kasa ya sauka zuwa 60, yanayi da ke buƙatar kulawa ta gaggawa. Ya ce ƙin ba shi hutun jinya ya ƙara taɓarɓarewar lafiyarsa ta jiki da ta kwakwalwa.
Akinlade na neman kotu ta ayyana cewa murabus ɗinsa ya fara aiki daga ranar da aka karɓe shi, tare da umartar rundunar ta biya masa fansho da duk wasu haƙƙoƙinsa, ganin cewa ya yi fiye da shekaru goma yana aiki. Haka kuma yana neman a ba shi damar kwashe kayansa na kashin kansa daga gidan da aka ba shi yayin aiki, tare da neman diyya ta naira miliyan 50 bisa zargin tauye haƙƙoƙinsa da jefa shi cikin damuwa, da kuma naira miliyan daya kuɗin shari’a.
A cikin jawabin lauyoyinsa, Akinlade ya jaddada cewa aiki a rundunar soja ba dole ba ne, hakki ne na ɗan ƙasa ya ajiye aiki idan ya ga dama. Ya ambaci Sashe na 306 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (da aka yi wa gyara), wanda ya tanadi cewa murabus na fara aiki ne da zarar an karɓi sanarwar rubuce. Ya buƙaci kotu ta tabbatar da cewa daga lokacin da aka karɓi murabus ɗinsa, rundunar ba ta da hurumin tilasta masa wani aiki ko ladabtar da shi.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Kotun Kwadago ta ƙasa ba ta sanya ranar fara sauraron shari’ar ba.
