Turmutsutsu: ’Yan sanda sun gargaɗi masu rabon abinci babu cikakken tsari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, IGP Kayode Egbetokun, ya yi gargaɗi kan raba kayan agaji ga jama’a ba tare da saamr da shirin na musamman ba a ƙasar.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Egbetokun ya gargaɗi masu shirya rabon tallafi cewa sakaci a ɓangarensu laifi ne.

IGP ɗin ya ce, “rashin ingantaccen tsari” na raba kayan tallafi ga jama’a a wasu yankuna a ƙasar ya haifar da ruɗani da turmutsutsu da bai zama dole ba.

A cikin sanarwar da ya fitar ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan Nijeriya, Muyiwa Adejobi ya ce; “Wannan gargaɗin ya biyo bayan jerin munanan al’amura da ke nuna buƙatar gaggawa na samar da tsari mai inganci da kuma hanyar isar da kayan agaji ga al’ummomin da ke da rauni da kuma jama’a gaba ɗaya.”

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 18 ga watan Disamba, 2024, wani lamari mai ban tausayi ya afku a garin Ibadan na jihar Oyo, inda aka samu wani turmutsutsu a wurin rabon tallafi wanda ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla yara 35 tare da jikkata wasu da dama.

Haka kuma, da sanyin safiyar ranar Asabar, 21 ga watan Disamba, 2024, wani bala’i ya afku a cocin Holy Trinity Catholic Church, Maitama, Abuja, a wani turmutsitsi makamancin haka da ya afku a lokacin rabon kayan abinci ga mabuƙata da tsofaffi, wanda ya kai ga rasuwar mutane 10, tare da jikkata wasu da dama.

Haka kuma irin wannan lamari ya afku a Okija, ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra, a wajen wani rabon kayan abinci da wani mai suna Obi Jackson ya yi, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane 12 ne aka tabbatar da mutuwarsu a safiyar ranar Asabar a garin Okija da ke ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra, a lokacin da suke fafutukar neman shinkafar Kirsimeti.

Sanarwar ta ce; “Wannan gargaɗin ya biyo bayan jerin munanan al’amura da ke nuna buƙatar gaggawa na samar da tsari mai inganci don isar da agaji ga al’ummomi masu rauni da kuma jama’a gaba ɗaya.

By ukarofi