Umarnin kotu muka bi ba samame ba, inji EFCC kan dirar mikiya gidan Malami na Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta bayyana hikimar da ta sanya jami’anta suka yi wa kadarorin tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami dirar mikiya, inda ta ce hakan yana ƙarƙashin doka da sahalewar umarnin kotu.

EFCC ta ce, abin da mutane da dama suka bayyana a matsayin samame, wani ɓangare ne daga cikin ayyukan da hukumar ke yi da umarnin ƙwace kadarorin na wucin-gadi daga wata babbar kotu.

Da yake magana a jiya Litinin, Kakakin EFCC Dele Oyewale, ya ce jami’an su kan sanya alamar bincike ne akan kadara don ankarar da al’umma cewa akwai batun shari’a a kai.

A cewarsa, sun ɗauki matakin ne bisa biyayya ga umarnin Babbar Kotun Tarayya na a ƙwace kadarorin tsohon antonin na wucin-gadi, yana mai cewa babu wani abu sabo ko wanda aka yi ba bisa doka ba.

Ya bayyana cewa, hakan gargaɗi ne ga jama’a cewa dukkan wata kadara da aka sanya wa tambari ko alamar hukumar, ana gudanar da shari’a akanta kuma akwai yiwuwar gwamnati ta ƙwace ta.

Kazalika, hukumar ta yi watsi da ikirarin cewa jami’anta sun kai samame gida ko ofishin Malami, inda ta bayyana hakan a matsayin abin da aka gina domin ruɗar da jama’a.

Hakan na zuwa ne yayin da wani faifan bidiyo ya karaɗe kafafen sada zumunta, wanda a ciki aka ga yadda ake musayar kalamai masu zafi tsakanin Malami da jami’an EFCC a wani wajen ɗaya daga cikin kadarorinsa.

By Babaji