Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Shirya Jarrabawar Yammacin Afirka (WAEC), ta sanar da fitar da sakamakon zango na biyu na jarrabawar WASSCE ta 2025 da aka gudanar ta hanyar kwamfuta ga masu zaman kansu, inda ta bayyana cewa an samu raguwar kashi 11.47 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Sanarwar da Shugabar Hulɗa da Jama’a ta WAEC, Moyosola Adesina, ta fitar ta ce kashi 42.17 cikin ɗari na ɗaliban da suka rubuta jarrabawar sun samu aƙalla darussa biyar da maki na kiredit, ciki har da Turanci da Lissafi.
Wannan adadi ya ragu daga kashi 53.64 cikin ɗari da aka samu a 2024, yayin da a 2023 aka samu kashi 44.29 cikin ɗari a irin wannan.
Daga cikin ɗalibai 65,752 da suka zauna jarrabawar, 27,727 ne suka samu darussa biyar da kiredit ciki har da Turanci da Lissafi. Sai dai hukumar ta jaddada cewa ba daidai ba ne a kwatanta sakamakon masu zaman kansu da na ɗaliban makarantu, domin jarrabawar masu zaman kansu ta ƙunshi mutanen da ba sa cikin tsarin makarantu.
Binciken sakamakon ya kuma nuna cewa ɗalibai 33,989, wato kashi 51.69 cikin ɗari, sun samu aƙalla darussa biyar da kiredit ko da ba tare da Turanci da Lissafi ba.
Jimillar zalibai 69,604 ne suka yi rajista a 2025, adadin da ya nuna ƙarin kashi 1.8 cikin ɗari idan aka kwatanta da 68,342 da suka yi rajista a 2024. Daga cikin masu rajistar, 65,752 ne suka rubuta jarrabawar a cibiyoyi 370 a faɗin ƙasa.
WAEC ta bayyana cewa sakamakon ɗalibai 61,943, wato kashi 94.21 cikin ɗari, an kammala sarrafa su kuma an fitar da su. Amma ɗalibai 3,809, kashi 5.79 cikin ɗari, har yanzu ana ci gaba da sarrafa wasu darussansu sakamakon kura-kurai da aka danganta da su.
Hukumar ta ce tana ƙoƙarin gaggauta kammala aikin domin a fitar da sauran sakamakon kam lokaci.
Haka kuma, dalibai 1,899, wato kashi 2.89 cikin ɗari, an dakatar da sakamakonsu bisa zargin aikata laifin satar amsa. WAEC ta ce ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma za a miƙa rahoto ga kwamitin da ya dace domin yanke hukunci, sannan a sanar da waɗanda abin ya shafa.
A ɓangaren jinsi, maza 32,005 ne suka rubuta jarrabawar, wanda ya kai kashi 48.68 cikin ɗari, yayin da mata 33,747 suka wakilci kashi 51.32 cikin ɗari. Daga cikin waɗanda suka samu darussa biyar da kiredit ciki har da Turanci da Lissafi, maza 13,416 ne (kashi 48.39), yayin da mata 14,311 (kashi 51.61) suka samu nasarar, lamarin da ya nuna ‘yan mata sun ɗan fi maza a wannan zangon.
An gudanar da jarrabawar tsakanin 11 ga Nuwamba zuwa 17 ga Disamba, 2025. Hukumar ta shawarci ɗalibai da su duba sakamakonsu ta yanar gizo domin tabbatar da matsayinsu, tare da sauke kwafin takardunsu ta dijital, yayin da za su iya neman takardar asali ta shafin takardun shaida na WAEC.
WAEC ta kuma sake jaddada ƙudurinta na ci gaba da bayar da ingantaccen aiki ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.
