
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya gargaɗi Gwamnan Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara kan yin rigima da magabacinsa na jagorancin jihar, Nyesom Wike.
A lokacin da ya ke magana a watan Mayu na 2023 a taron karrama Wike bayan ya miƙa mulki ga Fubara, Fayose ya bayyana cewa, Wike mutum ne da ba ya karɓar faɗuwa yayin da ake faɗa da shi.
Ya shawarci Fubara da cewa ya gudanar da harkokinsa cikin kulawa da ƙaurace wa abinda ya fi ƙarfinsa.
Fayose ya tabbatar da cewa ya san Wike a matsayin wanda idan ya ce zai yi faɗa da mutum, to sai inda ƙarfinsa ya ƙare ko kuma a miƙa wuya tare da sallama masa.
Bayan shekara ɗaya ne da waɗannan kalamai, aka samu Wike da Fubara a matsanancin rikici akan siyasar Ribas, wadda har ta kai ga Shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar da dakatar da gwamnan da mataimakiyarsa da Majalisar Dokokin jihar, tare da ɗora tsohon sojan ruwa VA Ibok-Ette Ibas a matsayin jagora.
