Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan sanda da sojoji sun ceto jami’in sojan ruwa da wasu da aka yi garkuwa da su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sanda da haɗin-gwiwar sojoji a Abuja, sun yi nasarar ceto wani jami’in sojan ruwa da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Mpape, ranar Juma’a.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta bayyana hakan a ranar Lahadi cikin wata takarda, inda ta ce a daren ranar ne aka samu wasu ƴan bindiga a yankin rukunin gidajen Maman Vasta da suka buɗe wa al’umma wuta tare da yin garkuwa da mutane ukun.

Jim-kaɗan bayan haka ne ƴan bindigar suka kira makusantan sojan, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 500 a matsayin kuɗin fansa sai kuma suka buƙaci miliyan N200 ga kowane ɗaya daga cikin suaran biyun.

Jin haka ke da wuya, Mataimakin kwamishinan ƴan sanda ɓangaren gudanarwa, DCP Isyaku Sharu ya nemi haɗa hannu da sojoji, inda daga nan ne suka gudanar da wani atisayen bin diddigi tare da gano maɓoyar ƴan bindigar da ceto mutanen a unguwar Mu’azu dake yankin duwatsun Yelwa a iyakar jihohin Abuja da Nasarawa.

Bugu da ƙari, sun ƙwato wasu kuɗaɗe kimanin Naira miliyan 3.2 daga hannun ƴan bindigar waɗanda ake zargin na fansa ne da suka karɓa a hannun mutane.

Haka kuma ana cigaba da bincike domin gano sauran waɗanda ake zargi da hannu a laifin, ta na mai kira ga al’umma da su kasance masu sanya ido game da abubuwan da ke faruwa a yankunansu tare da aiko rahoton dukkan wani abin zargi da suka gani ga hukumar ta lambobi kamar haka; 08032003913, 08028940883, 07057337653
08107314192.

By Babaji